Zaben 2023: Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mai Da Martani Ga ‘Yan Naija-Delta

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ‘yan yankin Naija-Delta, ta yi barazanar cewa dole ne yankin Arewa da yanzu haka ke mulkin kasar, ya jira har zuwa shekarar 2031, wato bayan shekaru 10 kenan, kafin ya sake samar da wani shugaban kasa.ABUJA, NIGERIA. — 

Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta sake gargadi ga masu da’awar cewa ya zama tilas mulkin kasar ya koma kudu a shekara ta 2023, wannan karon, tana mai da martani ne ga kungiyar ‘yan Naija-Delta.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ‘yan yankin Naija-Delta, ta yi barazanar cewa dole ne yankin Arewa da yanzu haka ke mulkin kasar, ya jira har zuwa shekarar 2031, wato bayan shekaru 10 kenan, kafin ya sake samar da wani shugaban kasa.

Sanarwar wadda sakataren yada labaran kungiyar ta ‘yan Naija-Delta na kasa, Ken Robinson ya fitar a birnin Fatakwal, ta ce bai kamata Arewa ta yi tunanin yin wani shugaban kasa ba bayan karshen wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na shekaru takwas.

To sai dai kungiyar dattawan Arewa ta jaddada matsayarta akan wannan cece-kuce, na cewa yankin ba zai lamincewa duk wata barazana kan shugabancin kasa ba, ta na mai cewa yin barazana kan lamarin ba zai haifar da da mai ido ba.

Dakta Hakeem Baba Ahmed, da ke zaman daraktan yada labarai da tallafawa na kungiyar, ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar kungiyar PANDEF da sauran kungiyoyi daga kudancin kasar ba su saurari matsayar Arewa ba kan lamarin a can baya, da ta bayyana cewa ba za’a yi mata barazana ko tsoratarwa daga wata kungiya ko yanki ba kan batun zaben shekarar 2023 ba.

Dakta Hakeem Baba Ahmed, daraktan yada labarai da tallafawa na kungiyar dattawan arewa.

Ya ce duk abin da wani yanki ko wata kungiya za ta fada, ya zama wajibi a mutunta hakkin kowane dan kasa na zaben dan takarar da ya ke so kuma a mutunta hakkin jam’iyyun siyasa na fitar da dan takarar da su ke so ya wakilce su a zaben kasa.

A cewar Baba-Ahmed, tsakanin wannan tanadin doka da ta ba wa yan kasa yancin zabe da wahalar tafiyarda alumma mai ɗimbin yawa kamar ta Najeriya, ya kamata ‘yan siyasa su yi aiki tukuru don cike gibin da ake samu idan ana maganar zabe.

“A shirye Arewa ta ke a zauna kan teburin tattaunawa ta yadda za’a iya yin sulhu kan wadannan maganganu da suka shafi zabe, amma ba za’a iya samun komai ta hanyar barazana. Arewa ta sha nanata matsayin nata sau da yawa, kar wanda ya yi wa Arewa barazana don hakan ba zai haifar da da mai ido ba,” in ji Baba-Ahmed.

Ya kara da cewa idan aka bi dokar kasa da tsarin mulkin dimokaradiyya za’a iya warware komai, amma muddin aka ci gaba da yin barazana ba bu inda za’a je.

Kungiyar arewa dai ta ba sauran kungiyoyi dake kiraye-kiraye kan shugabanci ya koma kudu shawara, da su dage kan fitar da dan Najeriya da ya kware, wanda zai iya gudanar da gwamnatin da za ta tafiyar da duk yan kasa a dukkanin ayyukanta bisa tsarin da ya kamata kawai, ba batun yanki ba.

-Source: VOAHausa-

One thought on “Zaben 2023: Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mai Da Martani Ga ‘Yan Naija-Delta

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.