Yanbindiga Sun Hallaka Akalla Mutane 4 tare da jikkata Wasu da Dama A Jihar Neja

Mahara dauke da manyan bindigogi akan babura sun auka a garin Gidigori a karamar Hukumar Rafi inda Bayan sun hallaka mutane sun kuma kona gidaje tare da yin garkuwa da wasu mutanen garin da dama,

NIGER, NIGERIA — Wani Mazaunin Yankin da ya bukaci a sakaya sunanshi ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ya zuwa lokacin da suke jana’izar wadanda maharan su ka kashe, mazauna yankin na cikin wani yanayi na tashin hankali.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kai wannan sabon hari,

A hirar shi da Muryar Amurka, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja Monday Bala kuryas yace su na kan tantance ainihin abinda ya faru. Bisa ga cewar shi, sun tura karin jami’an tsaro a yankin domin farautar maharan da kuma tantance lamarin.

Ya zuwa Lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga gwamnatin jihar Nejan akan wannan hari na garin Gidigorin,

-Source:VOAHausa-

One thought on “Yanbindiga Sun Hallaka Akalla Mutane 4 tare da jikkata Wasu da Dama A Jihar Neja

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.