‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Suka Jikata Sojojin Jamus Da Na Belgium A Mali

Majalisar Dinkin Duniya tace wasu sojojin Jamus 12 da wani sojan Belgium guda dake mata aikin kwantar da tarzoma a Mali sun jikata a jiya Juma’ a wani hari a arewacin kasar mai fama da tashin hankali.
Rundunar MDD a kasar ta MINUSMA a takaice, ta fara fadin cewa dakarun zaman lafiya 15 sun jikata a wata tungar wucin gadi dake yankin Gao da aka aunata da wata mota dauke da bam. Daga bisani ta gyara adadin.
Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer tace mutane uku a cikin sojojin sun ji munanan raunuka. Amma ta fadawa manema labarai a birnin Bonn na kasar Jamus cewa mutum biyu sun fara murmurewa yayin da na ukun ke samun kulawan gaggawa.
Kasar Mali ta yita kokarin dakile ayyukan kungiyoyin ta’adda masu ikirarin Musulunci tun cikin shekarar 2012.
Kungiyar ‘yan tawaye masu akidar tsaurin ra’ayi an tilasta musu barin mulkin biranen arewacin Mali da taimakon rundunar hadin gwiwa a jagorancin Faransa a shekarar 2013. Sai dai nan da nan kungiyoyin sun sake tattara kan su a cikin sahara uka fara kai hare hare a kan sojojin Mali da kawayen su a yaki da ‘yan ta’addan.
Kungiyoyin na masu tsaurin ra’ayi sun danna har cikin tsakiyar kasar Mali, inda shigar su ta haddasa tahin hankali tsakanin kabilun dake yankin.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.