‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Wani Dan Bindiga A Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, ta sami nasarar cafke wata mata mai suna, Aisha bafulatana, wacce a ke zargin mai dakin wani dan bindiga ne dake safarar bindigogi a jihar Katsina.ABUJA, NIGERIA. — 

Bayanai daga jihar Katsinan dai sun bayyana cewa, an kama matsar ne a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a lokacin da ta ke yin kokarin hawa babur din acaba domin zuwa kauyen Nahuta dauke da makudan kudadde.

A lokalin da aka sami nasarar kamata dai, Aisha Bafulatana na duake da tsabar nudi da aka kiyasta cewa, ya kai Naira miliyan biyu dubu dari hudu da biyar wato N2,405,000.00.

Hoton tsabar kudi da aka sama da matar wani dan bindiga a jihar Katsina.

‘Yan sandan jihar Katsina dake karamar hukumar Batsari dai sun sami nasarar kama Aisha Bafulatana ne biyo bayan samun bayanan sirri da rundunar ta yi a bakin wasu masu kishin kasa da bada taimako don kawo karshen ayyukan batagari.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kama barayin mutane da iyalan su da makudan kudadden ba a yankunan arewa maso yamma da ‘yan bendiga suka addaba.

Ana dai zargin cewa, Aisha Bafulatana, na dauke ne da kudadden da mijinta ya karbo a matsayin kudin fansa ko an bata kudin fansa ne ta aiwa mijinta a maboyarsa.

A cikin watan Yuli da ke karewa yau, wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne suka kai farmaki a was kauyukan jihar Katsina inda suka kashe kimanin mutane 19 wadanda yawancin su manoma ne a kauyen Tsauwa dake karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

An dai kwashe shekaru da dama ana fuskantar rikice-rikicen manoma da makiyaya lamarin da daga bisani ya rikide zuna ayyukan satar mutane domin neman kudin fansa.

Duk kokarin jin karin bayani kan wannan lamari daga bakin yan sanda a jihar ta Katsina ya ci tura a lokaci rubuta wannan labari.

-Source: VOA Hausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.