Gwamnatin Najeriya ta karawa jami’an ‘yan sanda albashi da kashi 20% da zai fara aiki daga watan Janairu na 2022.
ABUJA, NIGERIA — Hakan na daga cikin bukatu 5 da masu zanga zangar ENDSARS su ka gabatarwa gwamnati.
Ministan ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa na Ranar Larabar nan.
Dingyadi ya ce wannan yunkuri da aka yi na daya daga cikin bukatu 5 da masu zanga-zangar ENDSARS su ka gabatarwa gwamnati.

Ministan na ’Yan Sanda ya ce za a yi karin ne ta hanyar dada musu kudaden alawus-alawus dinsu da kaso shida cikin 100, da kuma karin Naira biliyan 1.1 don biyan basussukan da suke bi na tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce za a kara albashin ne don ya dace da ayyukan da suke yi da kuma karfafa yunkurin samar da zaman lafiya a kasa.

annan ya nuna duk jami’an ‘yan sanda a fadin kasar za su samu karin akalla kashi 20% na albashin da su ke karba a yanzu.
Ba mamaki wannan ya rage korafin ‘yan sandan na rashin ingancin albashi da ma kudin fansho bayan ritaya daga aiki.
Rahoton ENDSARS: Wata Karyar Ce Kawai Aka Tsara Inji Gwamnatin Najeriya
Ana Zargin Wani DPO Da Yin Amfani Da Tabarya Wajen Azabtar Da Mutane
Masu kula da lamura na kuma kyautata zaton karin albashin zai rage cin hanci da rashawa da ake zargin wadansu jami’an ‘yan sanda da aikatawa da ake dangantawa da rashin kyaun tsarin kula da ‘yan sanda.
Bayan zanga zangar da aka gudaar a birane da dama na Najeriya da ya sami asali daga gangamin da matasa su ka fara a birnin Lagos na neman kawo karshen gallazawa al’umma da jami’an ‘yan sanda su ke yi da kuma neman kudi da karfi da yaji a hannun wadanda su ka kama, matasan sun ba gwamnati zabi kan matakan da za a dauka kafin su daina zanga zanga da suka hada da karawa jami’an ‘yan sanda albashi da kuma daukar matakan mutunta aikin da inganta rayuwarsu.

“Tsabar Azaba Ta Sa Ni Amsa Laifin Da Ban Aikata Ba” – Matashi
Ana Zargin Wani DPO Da Yin Amfani Da Tabarya Wajen Azabtar Da Mutane
#EndSARS: Sojoji Sun Bada Bahasi Gaban Kwamitin Bincike
-Source:VOAHausa-