Al’ummar Owo da ke jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya ba za su taɓa mantawa da harin da ya auku a ranar 5 ga watan Yuni ba, inda ‘yan bindiga suka shiga garin sannan suka kai hari cocin St Francis Xavier.
Mahukunta ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba, amma ziyarar da BBC ta kai wani asibitin gwamnati a Owo ta nuna yadda mutane da dama suka jikkata.
Fafaroma Francis da Shugaba Muhammadu Buhari na cikin mutanen da suka yi Allah-wadai da wannan kazamin harin.
‘Yan sanda a jihar sun ce sun kaddamar da bincike kan al’amari.
‘Na tsinci gawar ɗan uwana da ɗansa cikin kazamin yanayi a cocin’
Wani mutum da ya ce ɗan uwansa da ɗansa sun mutu a harin ya shaida wa BBC yadda ya samu labarin mutuwar tasu.
Cletus Okarfor ya ce ya karɓi sako a wayarsa da ke sanar da shi cewa an kashe ɗan uwansa bayan dawowa daga coci a ranar Lahadi.
Ya ce nan take ya gaggauta rugawa cocin, kawai sai ya iske ɗan uwan nasa, mai shekara 40, da ɗansa mai shekara uku, Chisom, cikin jini.
“Bayan mun tashi daga coci a ranar Lahadi, shi ne sako na farko da ya shigo wayata, da ke sanar da ni cewa an kashe ɗan uwana a cocin St. Francis Owaluwa, nan take cikin gaggawa na isa inda abin ya faru, ina isa wurin na iske gawarwakinsu da na ɗansa a kasa.
“Daga nan na tsara yadda mota za ta kai su mutuware”
Ya ce an harbi ɗan uwan nasa a kirji, ɗansa kuma a kafa da kai.
Kungiyar Likitoci ta NMA ta bukaci gudunmawar jini
Ƙungiyar likitoci ta NMA ta yi kira da a taimaka wa wadanda suka jikkata da jini.
A wata sanarwa da Shugaban NMA, Dakta Uche Ojinmah, ya fitar sa’o’i bayan harin ya ce ana cikin wannan bukata ta gaggawa.
Ya ce “muna roƙon ‘yan Najeriya mazauna yankin da abin ya faru a jihar Ondo su je asibitin da aka kwantar da mutane, domin tallafa musu da jini don ceto rai”.
Dakta Ojinmah ya yi kira ga likitocin jihar su shirya kansu domin gudanar da tiyata kan mutanen da aka jikkata.
Wannan na zuwa ne a yayin da suke sukar gwamnati kan rashin daukar mataki game da yawaitar zub da jini a kasar.

-Source: VOAHausa-