Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Layin Dogo A Hanyar Kaduna: Ganau

Daya daga fasinjojin jirgin kasan da mahara su ka kai wa hari kan hanyar Abuja zuwa Kaduna Abdulwabid Ahmad ya ce bayan harin sojoji sun zo inda su ka taimaka masu su ka hau wani tsauni gabanin jigilar su a mota zuwa tudun mun tsira.

KADUNA, NIGERIA – Abdulwabid Ahmad ya bayyana cewa bayan dasa nakiya da ta kayar da jirgin, barayin sun yi musayar wuta da jami’an tsaron da ke raka jirgin, inda su ka fi karfin su har su ka kutsa cikin jirgin su na harbe-harbe da kuma ya kai ga sace fasinjoji da dama.

Fasinjan ya ce zuwa lokacin da Muryar Amurka ta yi hira da shi, an kirga mutum 9 da su ka rasa ran su ciki har da direban jirgin, inda wasu kuma su ka samu raunuka.

Ahmad ya ce shi ma a karkashin kujera ya buya ya na addu’a har lamarin ya lafa bayan an harbe wani fasinja a taragon da su ke ciki.

Hakanan ya ce maharan sun je da motoci su ka jidi mutane su ka kutsa cikin daji.

Sojoji, a cewar fasinjan, sun bukaci fasinjojin su kashe fitilar wayoyin su, da rage surutu har aka samu aka kubutar da su daga yankin mai hatsari.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.