Watford 0-5 Liverpool: Claudio Ranieri ya sha kashi wasansa na farko a Watford

Kwallaye uku Roberto Firmino ya ci a wasan da Liverpool ta lallasa Watford, wasan farko da Claudio Ranieri ya jagoranci kungiyar a gidanta.

Liverpool ta doke Watford ne ci 5-0.

Sadio Mane ya zama ɗan wasan Afirka na uku da ya ci kwallo 100 a Premier inda ya fara zura kwallo kafin Roberto Firmino ya ci Watford.

Mohamed Salah ne ya ci ƙwallo ta hudu da ta kayatar a wasan bayan ya yanke masu tsaron baya kafin uya jefa kwallon a ragar Watford.

Salah yanzu ya yi kafada da Didier Drogba a matsayin ƴan wasan Afrika da suka ci cin ƙwallaye a gasar Premier League da ƙwallo 104.

Firmino ne ya rufe da ƙwallo ta biyar ana dab da hure wasan, karon farko da ya ci kwallo uku rigis tun watan Disamban 2018.

Sakamakon ya nuna Liverpool ta ci kwallaye uku ko fiye a wasanninta shida da ta buga a waje a kakar bana.

Har yanzu ba a doke Liverpool ba a bana. Yanzu ta ɗare tebur kafin Chelsea ta kai wa Brentford ziyara.

Tun da aka fara wasan Watford ba ta buga kwana ba sai ana minti 78 da wasa, wani abin da ya ja hankalin ƴan kalo musamman a ranar farko da Ranieri ya jagoranci ƙungiyar.

Watford ce kungiya ta 22 da Ranieri ya jagoranta a tarihinsa na horar da ƴan wasa.

Wannan ne sakamako mafi muni da Watford ta sha kashi tun dukan da Manchester City ta yi mata a watan Satumban 2019.

-Source:BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.