Wata Kungiyar Da’awar Kishin Kasa Ta Yi Taron Bunkasa Dabi’ar Kishin Kasa A Tsakanin ‘Yan Najeriya

Kungiyar da ke tuna tarihi lokacin da a ka hade kudanci da arewacin Najeriya a 1914, ta ce wasu maso son zuciya da kuma musamman masu fakewa da bambance-bambance don cimma muradun siyasa.

WASHINGTON DC — Taken taron dai shine dawo da kishin kasa ta hanyar aikin sa kai don magance matsalar rashin aiki a Najeriya.

Kakakin kungiyar Komred Salihu Dantata Mahmud ya ce wadanda su ka yi gwagwarmayar karbo ‘yancin Najeriya sun dora jama’a ne kan zaman tare da taimakon juna.

Komred Dantata ya ce daga bisani wasu su ka nemi sauya dabi’un don cimma muradun son zuciya.

Hatta masu son raba kasa da kawo bambancin addini da kabilanci duk sun sauka daga turbar da iyayen Najeriya su ka dora kasar.

Mataimakin shugaban kungiyar Kabir Ishaq Sa’id ya ce abunda ake so cimma shine dawo da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al’umma.

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da mai wakiltar matasan kiristoci na Najeriya Ambasada Love Sheyin da Alhaji Muhammad Maijajere sunce shirya irin wadannan tarukan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da cigaban kasa.

A dai dai lokacin wasu kabilu ke neman ballewa a Najeriya Kungiyoyi da dama sun tashin tsaye don ganin an zama tsinstiya madaurinki daya.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.