Wani Dan Fafutuka Ya Rasu Bayan Da Wasu Mutane Suka Kai Masa Hari

Wani dan shekaru 40 da ya samu raunukan sara a kansa a wani hari da aka kai masa a garin Ejura a yankin Ashantin Ghana a ranar Asabar, ya rasu jiya Litinin da rana a asibitin koyarwa na Komfo Anokye a Kumasi.

Babban likita a asibitin gwamnati dake Ejura, Dr. Mensah Manye ya fadawa manema labarai cewa Mohammed mai inkiya Kaaka ya samu rauni mai muni a kansa kana ya zubar da jinni da yawa.

Wasu mutane biyu da ba a gane ko su wanene ba wanda ‘yan sanda ke farautar su ne suka kai masa hari.

An kai masa sara sau da yawa a kansa har sai da ya fita cikin hayyacin sa.

A lokacin da aka isa da shi a asibiti, Mohammed baya iya karbar jinya saboda irin raunuka da ya samu.

Dr. Manye ya ce dole ne ya tura shi zuwa asibitin koyarwa na Konfo Anokyi a Kumasi domin bashi kulawar da ta dace.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa tun da aka kai shi asibitin ne aka dor masa na’urar nunfashi na “oxygen” har sai da ya cika a jiya Litinin da misalin karfe 1:30 na rana.

Mambobin kungiyar fafutukar inganta tattalin arziki ta Economic Fighters League (EFL) da suke kai-komo a kan halin da Mohammed ke ciki sun bayyana matukar damuwar su ga wannan lamari.

Shugaban kungiyar Fighter-General, Hardi Yakubu, ya yi kira ga ‘yan sandan Ghana da su yi duk iya bakin kokarin su su kamo wadanda suka yi wannan aika aika.

“Ya kamata duk ‘yan Ghana da mutane masu sanin ya kamata su tashi tsaye su amsa kirar mu.”

Ya ce ba zasu kyale mutuwar mutumin da bai aikata wani laifi ba ta tafi ba tare da bi masa kadi ba.

“An kashe Kaaka ne saboda yana bukatar a gayara Ejura da kuma gyara Ghana. Toh menene laifin sa? Fight-General Yakubu yana tambaya.

Iyalai da abokai suna jimamin mutuwar dan uwan su da suka yi imani yana kira ne kawai zuwa ga kyautata rayuwar mutanen sa.

Suna so ‘yan sanda su yi abin da ya dace.

-Source: Myjoyonline-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.