Varane zai yi jinyar wata daya

Mai tsaron bayan Manchester United Raphael Varane zai shafe kusan wata daya yana jinya.

Varane ya samu rauni a wasan zakarun Turai da United ta tashi 2-2 da Atalanta na Italiya.

Dan Faransan mai shekaru 28 ya tafi United daga Real Madrid kan fam miliyan 34 a watan Agusta, kuma bai jima da dawowa daga wani raunin ba.

Jinyar da Varane zai yi na nufin ba zai buga wasannin Premier League da kulob dinsa zai yi da Manchester City da kuma Chelsea ba.

Shima mai tsaron baya Victor Lindelof bai samu tafiya Italiya wasan Atalanta ba saboda rauni, gashi kuma tauraruwar kyaftin din kungiyar Harry Maguire ta fara dusashewa.

-Source:BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.