Tokyo Olympics: Ministan Wasanni Ya Karfafa wa ‘Yan Wasan Ghana Kwarin Gwiwa

Ministan matasa da wasanni na Ghana Mustapha Ussif ya yi kira ga ‘yan wasannin Ghana da suke wakiltar kasar a gasar duniya ta Olympics da su yi amfani da wannan dama da suka samu ta zuwa gasar wajen daukaka sunayensu da na kasarsu.WASHINTGTON D.C. — 

Yanzu haka ministan na can kasar Japan ne bisa gayyatar kwamitin Olympics na kasa da kasa, inda ya gana da ‘yan wasan kana ya mika masu sakon fatar Alheri daga shugaban Nana Addo Dankwa Akufo Addo da baki dayan al’ummar Ghana.

“Ina mika muku sako na musamman daga shugaban kasa Akufo Adda da mutanen Ghana baki daya. Ina tabbatar muku cewa al’ummar kasa suna tare da ku saboda kuna baiwa kasar mu wakilci kana zaku daukaka tutar kasar sama,” Mustpha Ussif yana fadawa ‘yan wasan.

Ya kuma karfafa gwiwar su da su taka rawar gani a gasar da ya kwatanta da ta musamman.

Gasar Olympic wani biki na musamman ga kowane dan wasa a duniya kana mafarkin kowan dan wasa ne ya shiga wannan gasa, shi yasa ku yi alfaharin cewa kun samu shiga wasannin.

Ku zage damtse, ko da yake, kuna wasannin ne a cikin filin da yake fayau ba ‘yan kallo, amma ku sani cewa duk mutanen Ghana a gida na bibiyar ku.

Ministan matasa da wasannin yana cikin jami’an Ghana kalilan da aka basu damar kusanta da ‘yan wasan jiya Litinin yayin da dan damben boxing Ghana Suleman Tetteh ya lallasa abokin karawarsa dan kasar Jamhuriyar Dimnican, Marte Rodrigo, ya yi nasara a kansa.

A ranar Laraba ne wasu ‘yan wasan Ghana za su yi wasanninsu, ministan ya gargade su da sauran wakilan Ghana da su dubi nasarar da Suleman Tetteh ya yi su kuma su taka rawar gani.

Ministan dai ya nuna sha’awar raya duk fnnonin wasa a Ghana tun lokacin da aka nada shi ya kama aiki, dalili kenan kuma da yasa yake bibiyan ayyukan kwamitin Olympic na cikin gida da kuma kungiyoyin dake karkashin sa omin basu duk taimakon da suke bukata.

A wannan takaitaccen ziyarar, ministan ya gana da jami’an kwamitin Olympic na kasa da kasa da kuma shugabnnin kungiyoyin dake karkashin su da takwarorinsa ministocin wasanni da ma Mustpha Barraf da Hashi Ahmed.

Shugba da kuma babban sakataren kwamitin Olympic na Afrika domin tattauna batutuwan hadin gwiwa na raya wasanni da kuma shirye shiryen da Ghana ke yi na daukar nauyin shirya Gasar wasannin Afrika.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.