Tashin hankali na karuwa a Sudan kan kafa gwamnatin farar hula

Firai ministan Sudan Abdallah Hamdok, ya yi gargadi kan kokarin da wasu ke yi na kawo cikas a kan tafiyar da harkokin mulkin gwamnatin hadaka, a dai dai lokacin da ake samun karuwar tashin hankali tsakanin sojoji da farar hula.

An kafa gwamnatin ne bayan hambarar da mulkin shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019, wanda ya shafe gwamman shekaru ya na mulkar kasar.

A watan da ya gabata dai an yi yunkurin juyin mulki a Sudan din, amma ba ai nasara ba, haka kuma rufe daya daga cikin tashar ruwan kasar ta kara jefa Sudan cikin matsin tattalin arziki.

Hamdok, ya ce hanya daya tilo da ta rage wajen kaucewa abin da ya kira fadawar kasar cikin hadarin rikicin siyasa ita ce hawa teburin sulhu domin sasantawa.

Sai dai ya san cewa har yanzu akwai gaggan sojin kasar masu karfin fada aji dake burin ganin sun kassara shirin kafa gwamnatin farar hula a Sudan.

Tun dai bayan yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a watan da ya gabata, ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula da musayar yawu a majalisar ministocin kasar da kuma farar hula.

Ana dai hasashen kwanaki masu zuwa ka iya zama ma su tsauri da haddasa halin zaman dar- dar da rashin tabbas a kasar.

‘Yan siyasa sun yi kiran a fito zanga-zanga a ranar Lahadi domin nuna adawa da gwamnati mai ci.

Ya yin da aka shirya wata sabuwar zanga-zangar a ranar Alhamis din mako mai zuwa, wadda ita kuma ta kiran a kafa gwamnatin farar hula ce.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.