Shin tallafin Burtaniya na iya taimakawa Najeriya kawo ƙarshen matsalolin tsaronta?

Firaiministan Burtaniya Boris Johnson ya ce ƙasarsa a shirye ta ke ta taimaka wa Najeriya kan matsalar tsaro da ke damunta.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar ta ce, Boris Johnson ya bai wa shugaba Buhari wannan tabbaci ne a gefen taron haɓɓaka ilimi da ke gudana a Landan.

Bayan dogon nazari da shugabannin suka yi wa matsalar tsaron ƙasar, sun amince da cewa dole a kyale ɓangaren shari’a ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Duka shugabannin sun yarda cewa dole a kyale shari’a ta rika aikinta ba tare da katsa-landan ba, kuma ko da wanene shari’ar ta shafa.

Buhari ya kuma yi wa Firaiministan bayani a takaice kan ikon da Najeriya ke bukatar samu da kuma ƙoƙarin da take yi na tabbatar da ta samar da abincin da za ta iya rike kanta da shi.

Ya kuma yi masa bayanin matsalar tsaron da yankunan Najeriya ke ciki, ɓangaren arewa maso gabas Boko Haram, arewa maso yamma na fama da ‘yan fashin daji arewa ta tsakiya na fama da masu garkuwa da mutane.

Ya kuma bayyana masa a kudancin Najeriya ana fama da yunkurin ɓallewar ‘yan Biafra da kuma ƙasar Yarbawa.

Wane irin taimako Najeriya ke buƙata ?

‘A sanya matasa su shagaltu da karatu da kuma samar musu da sana’o’i da za su sanya su mayar da hanakali a kan gina rayuwarsu, su manta da ayyukan ta’addanci.’

“Akwai taimako kamar kala uku da Najeriya ke buƙata” in ji Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi kan harkokin tsaro

Cikin wata tattauna wa da BBC ta yi da shi, Bulama ya ce akwai taimako na ɓangaren soji, da na ‘yan gudun hijira da kuma na sanya kuɗi wajen ilimi.

Waɗannan manyan taimako za su iya zama na yanzu-yanzu da wadanda na gajeren zango ne da na dogon zango.

Dukkansu za su iya kawo babban sauyi ga halin da Najeriya ke ciki.

Taimakon soji

“Taimakon da ake bukata na soji, taimakon yanzu-yanzu ne yadda za a tunkari abokan gaba a filin daga.

Da taimakon soji za a iya ƙara bai wa shugabannin sojojin Najeriya horo da ƙwarewa wajen fuskantar wadanda ake yaƙi da su.

Ƙwarewa ta fuskar karɓar bayanai, iya sarrafa sabbin kayan aiki da kuma wasu fannonin da sojoji ke buƙatar ƙwarewar aiki.

Akwai taimakon kayan aiki da sojin Najeriya ke buƙata, “mafi yawan kayan aikin da ake yaƙi da su sun tsufa ta fuskar cewa zamaninsu ya shuɗe.

“Wadannan mayakan da ake tunkara za ka ga suna amfani da sabbin kayan aikin da ko a Tuarai da irinsu ake yaƙi a yanzu, to sojojin Najeriya na buƙatar irinsu,” in ji Bulama

Taimako ga ‘yan gudun hijira

Dubban ƴan gudun hijira a Najeriya na cikin halin yunwa babu wajen kwana mai kyau babu magunguna mai kyau.

Kuma duka waɗannan dalilin yunwa ne da rashin magani mai kyau da rashin samun wurin kwana mai kyau,” in ji Barista Bulama.

Akwai matsalar cin zarafi da rahotanni ke ambato wa game da ‘yan gudun hijira a Najeriya, kuma wannan yana shafar yara mata a wasu lokutan har da iyayensu.

Bulama ya ce mafi yawan waɗannan yara sun bar zuwa makaranta wanda hakan barazana ce ga rayuwarsu ta gobe da suke fuskanta.

Taimakon gajere da dogon zango

Wannan taimakon ya fi karfi a maganar sanya kuɗi a bangaren ilimi da kuma tattalin arziki.

A sanya matasa su shagaltu da karatu da kuma samar musu da sana’o’i da za su sanya su mayar da hanakali a kan gina rayuwarsu, su manta da ayyukan ta’addanci.

Cikin taimakon da Burtaniya za ta iya yi wa Najeriya a yanzu shi ne ta taimaka mata da kayan aiki a gano inda waɗannan mutane da ake yin wannan fada da su suke.

Mai yasa ƙasashen duniya ke zargin Najeriya da take haƙƙin dan adam?

Amurka da Burtaniya na zargin Najeriya da take hakkin dan adam ta fuskar soji, kuma wannan abu ne da suke yi a buɗe da zai iya jawo tsaiko ga taimakon da suke shirin bayar wa.

Barista Bulama ya ce: “A 2017 Firaiministan Burtaniya Boris Johnson ya yin wata ziya da ya kai Maiduguri babban birnin Jihar Borno, ya ce yana ganin kuɗaɗen da Burtaniya ke bai wa Najeriya na agaji ana kashe su ne ta fuskar muzgunawa abokan gaba maimakon yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ta’addanci.

“Bayan nan ‘yan majalisun Burtaniyan sun yi korafin cewa ana take hakkin bil’adama a Najeriya,” wanda kuma wannan nauyin gwamnati ne na ganin ta jajirce an bi duk ƙa’idoji in ji Bukarti.

-Source: BBC Hausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.