Fitaccen malamin addinin musulunci na Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya faɗi dalilan da suka ya gina makaranta da asibiti da kuma wajen koyar da sana`a ga al`ummar Fulani makiyaya da ke yankunan karkara a jihar Kaduna.
Malamin ya shaida wa BBC cewa ya gina Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio ne a garin Kagarko, a kusa da gandun dajin Kohoto da ke jihar ta Kaduna domin ilmantar da makiyaya.
A cewar Malamin ilimantar da makiyaya da samar musu da abubuwan more rayuwa ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya.
Ɗa’awar da malamin ya ƙaddamar ta shiga dazuzzukan da ƴan bindiga ke yin mafaka yana yi musu wa’azi da kira gare su su ajiye makamansu ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda wani ɓangare na ƙasar ke sukar matakinsa a matsayin nuna goyon baya ga munanan ayyukan da suke aikatawa.
Ya sha cin karo da hukumomi da kuma wasu ƴan ƙasar kan batun matsalar makiyaya da ake zargi suna fashi da satar mutane domin kuɗin fansa.
- Kungiyoyin Kwadago Sun Bukaci Buhari Ya Ceto Cibiyoyin Bincike Daga Durkushewa
- Sarkin Bauchi Ya Tsige Wasu Sarakuna Hudu Bisa Zargin Taimaka Wa ‘Yan Ta’adda
- NIJER: Matsalar Tsaro Ke Ta Addabarmu- Bazoum Mohamed
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƙarancin ilimi na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin arewacin Najeriya.
Wannan na daga cikin dalilin da malamin ya bayyana kan ƙaddamar da wani gangami na fita yankunan jihar Kaduna da ma wasu jihohin domin ilimantar da mazaunansu da kuma yi musu wa’azi.
Ya ya gano matsalolin makiyayan ne ta hanyar mu’amular da ya yi da su lokacin da yake shiga daji domin yi masu wa’azi.
-Source:BBCHausa-