Senegal Ta Lashe Kofin Gasar AFCON A Karon Farko

An ga Mane da ya buga fenariti ta karshe da ta ba Senegal nasara, yana ba Salah hakuri bayan da aka kammala bugun fenaritin.

WASHINGTON D.C. — A karon farko, Senegal ta lashe kofin gasar cin kofin nahiyar Afirka bayan da ta doke takwararta ta kasar Egypt a wasan karshe.

Senegal ta samu nasarar ce da ci 4-2 a bugun fenariti da aka yi bayan da bangarorin biyu suka gaza cin kwallo a mintina 120 da aka kwashe ana wasan.

Senegal ta kai wasan na karshe ne bayan da ta doke Burkina Faso a wasan kusa da na karshe a makon da ya gabata da ci 3-1.

Ita kuwa Egypt wacce ta taba lashe kofin gasar sau bakwai, ta doke Kamaru ne a wasan gab da na karshe da bugun fenariti.

Wasan ya ja hankali masoya kwallon kafa da dama a duniya, la’akkari da cewa ya hada shahararrun ‘yan kwallon kungiyar Liverpool, wato Sadio Mane da dan wasan Egypt Mohamed Salah.

An ga Mane da ya buga fenariti ta karshe da ta ba Senegal nasara yana ba Salah hakuri.

Bangarorin biyu musamman Senegal, sun yi ta kai wa hare-hare yayin wasan, wanda aka buga a filin wasa na Olembe da Yaounde, babban birnin Kamaru.

A ranar Asabar Kamaru ta lashe matsayi na uku bayan da ta doke Burkina Faso da bugun fenariti.

Wannan shi ne karo na 33 da ake buga gasar wacce Kamaru ta karbi bakuncinsa.

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.