Rashin Hukunci Ya Sa Jami’an Tsaro Watsi Da Umurnin Buhari – Masana

Yawan umurnin da shugaban kasar Najeriya ke bayarwa na kawar da ayyukan ‘yan bindiga bai sa suka daina ta’asarsu ba a sassan kasar daban-daban.

SAKKWATO, NAJERIYA — A wannan karshen mako ma sai da suka kashe mutane shida tare da kona shaguna da satar dabbobi da mutane a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar.

‘Yan Najeriya sun jima suna jin irin wannan kalami daga Shugaba Muhammadu Buhari, sai dai har yanzu da yawa suna zaman zullumi, domin umurnin ya kasa yin tasiri a yankunansu.

Mazauna garin Masasa a karamar hukumar Illela ta Jihar Sakkwato shaidu ne akan rashin tasirin wannan umurnin, domin a ranar Asabar da ta gabata, sun dauki bakuncin ‘yan bindiga a garin su.

Wakilin su a majalisar dokoki ta jiha, Bello Isa Ambarura, ya ce sun kashe mutane shida tare da kwashe dukkanin kayan shagunan garin Masasa da dabbobi, da suka hada da shanu da awaki wadanda ba’a san adadin su ba.

Ya kara da cewa sun tafi da mutane da har yanzu ba’a san adadin su ba kana mutane garin duka sun waste inda wasu suka tsallaka kauyukan da ke kusa da garin.

Wani Mazaunin Illela kuma tsohon kansilan Kalmalo, Hamza Kalmalo, ya ce yanzu mutane da suka rage a garin daidaikune kuma jami’an tsaro sun isa garin sai dai babu wani abu da suke yi, inda talakawa ne ke tsare kan su.

Duk da nasarorin da ake nuna cewa sojoji na samu akan ‘yan ta’adda wasu lokuta, jama’a na ci gaba da mamakin yadda har yanzu umurnin da shugaban Najeriya ya jima yana bayarwa bai kawo karshen wadannan matsalolin ba.

Masu sharhi akan lamurran yau da kullum na ganin akwai dalilin da ya sa umurnin da ake ta bayarwa ya kasa tasiri.

A hirar shi da Muryar Amurka, Farfesa Bello Badah na Jami’ar Usmanu Danfodiyo ya ce gidan yari na Kuje da aka fasa suka kwashe duk mutanensu babu wani mutum guda da aka hukunta kan wannan al’amari. Kuma idan shugaba kasa ya bawa sojoji umurni ayi kaza ayi kaza kana har lokacin ya cika ba’a yi ba, ba’a yiwa kowa komai, to da zarar ya zamo ba’a hukuntar da wanda ya yi laifi ba, to sam tsoro na shugaban kasa ya fita daga zukatansu, idan ya bada umurni sai su yi abin da suke so su yi.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin jami’an tsaron Najeriya akan wannan harin na Illela ya ci tura.

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.