Rasha Na Fuskantar Karin Takunkumi A Fagen Wasanni

Ana kara saka takunkumi akan ‘yan wasan Rasha a wasanni daban-daban da ake yi a sassan duniya a daidai lokacin da mai kulob din Chelsea ya saka ta a kasuwa.

WASHINGTON, D.C. — Ana kara saka takunkumi akan ‘yan wasan Rasha a wasanni daban-daban da ake yi a sassan duniya a daidai lokacin da mai kulob din Chelsea ya saka ta a kasuwa.

Wasan tebur tennis na daya daga cikin gasar da aka haramtawa Rasha shiga baya ga wasu jerin wasanni a gasar Olympics.

Sai dai ba a hana ‘yan wasan na Rasha shiga gasar wasannin masu nakasa ba na paralympics ba.

Hukumar da ke shirya gasar wasannin Olympics ta nasassu ta ce ‘yan wasan Rashar da na Belarus za su iya shiga gasar amma a matsayin daidaikun ‘yan wasa masu zaman kansa ba a karkashin Rasha da Belarus ba.

Amma an haramtawa kasar shiga gasar kwallon kafa, wasannin tsalle-tsalle, kwallon Kwando, wasan kokara ta hockey da sauransu bayan da kasar ta mamaye Ukraine.

Gasar ta Paralympics za a fara ta ne a ranar Juma’a a kasar China, kuma tuni ‘yan wasan Rasha da dama sun isa Birnin Beijing don karawa a gasar.

-SourceVOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.