Ranar abinci ta duniya wato 16 ga watan Oktoba, ta wannan shekara ta zo a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargadi na gagarumar matsalar karancin abinci da fargabar hauhawr farashin kayan abinci a duniya.
“Kusan mutane rabin miliyan na fama da abin da za a iya cewa ya kai na gagarumar yunwa a Ethiopia da Madagascar da Sudan ta Kudu da Yemen. A ƴan watannin nan, talakawa a Burkina Faso da Najeriya sun sun shiga irin wannan yanayi,” in ji wata sanarwa ta Majalisar Dinkin Duniya.
Dangane da hakan Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kira da a gaggauta samar da kudade ga mutane miliyan 41 d ke cikin hadarin fadawa wannan yanayi na yunwa.
A bisa bayanai da alkaluman wata kungiya mai cibiya a Birtaniya, (The Hunger Project), yayin da mutane miliyan 690 a fadin duniya ke fama da tsananin yunwa, wasu miliyan 850 mutanen na hadarin fadawa fatara da talauci saboda korona. Daga cikin wadannan miliyan 690 kashi 60 cikin dari mata ne.
To a nan mun duba abin da wannan matsalar ta tashin farashin kayan abinci ke nufi a zahiri ga mutane a faddin duniya, da kuma hanyoyin da za a bi domin maganinta.
Da farko bari mu duba dalilan da ke janyo hauhawar farashin kayan abincin.
Me ya sa farashin ke tashi?

Katafaren kamfanin nan na abinci na duniya, Kraft Heinz, ya yi gargadin cewa dole ne mutane su yi hakuri da yadda farashin kayan abincin ke tashi saboda matsala ce ta hauhawar farashi ta bayan annobar korona.
Dr Sarika Kulkarni, wadda ta kafa gidauniyar Raah Foundation, da ke Mumbai, a India, ta yarda da ra’ayin Miguel Patricio, shugaban kamfanin na Kraft Heinz, wanda ya ce farashin ya ci gaba da tashi ke nan.
Dr Kulkarni da gidauniyar Raah Foundation na aiki domin inganta rayuwar talakawa a India.
A lokacin annobar korona kasashe da yawa sun samu raguwar ayyukan samar da kayayyakin da ake sarrafawa, kama daga kayan amfanin gona da ake yin kayan abinci da su da man girki. Matakan dakile cutar da rashin lafiya sun rage yawan kayayyakin da ake samarwa da kuma takaita kaiwar.
Yayin da kasashe da kamfanoni suka sake dawowa samar da wadannan kayayyaki, da dama daga cikinsu ba sa iya biyan yawan bukatar da ke da ita ta kayayyakin, wanda a dalilin hakan farashi ke tashi.
Biyan albashi mai yawa da farashin makamashi su ma sun kara nauyi ga masu yin kayayyakin.
”Tarin matsalolin da manoma ke fuskantsa wadanda ake gani a matsalar ta tashin farashin kayan abinci su ma na ci gaba da karuwa.” A cewar Dr Kulkarni.
‘Mata na bayar da kansu domin samun abinci’

Kamar yadda mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan jin-kai, Martin Griffiths ya ce: “Idan yunwa ta durfafo cikin al’umma, ta kan bazu yadda wasu matsalolin ma ba sa yi.”
Mata da ƴan mata sun fi shiga hadari ko raunin fadawa wanan matsala sakamakon karuwar fatara da talauci da ktashin farashin kayan abinci.
”Mata na fada mana irin tsananin abubuwan da suke yi da matakan da suke dauka wadanda suka zamar musu dole domin samun abincin da za su ciyar da iyalansu. Hakan ya hada da bayar da kansu ga maza domin su samu abinci, da yi musu auren wuri da aurar da yara suna kanana, kamar yadda nake ji lokacin ina Syria a kwanan nan,” in ji shi.
Wasu daga cikin mutanen da wanan matsala ta fi shafa a duniya su ne kananan manoma, in ji Karen Hampson, babban jami’in shirye-shirye a gidan rediyon manoma na Farm Radio International.
Ya ce halin da ake ciki yanzu dangane da tsadar kayan abinci, abu ne mai fuska biyu, a bangare daya iyalai manoma suna bukatar sayen nau’in abincin da ba su suke nomawa ba, ta nan tsadar na shafarsu abin da zai iya kai su ga yunwa da rashin samun abinci mai gina jiki wadatacce.
A daya bangaren kuwa tsadar abincin wata dama ce a wurinsu ta samun karin kudi idan ana maganar nau’in kayan abincin da su suke nomawa. To amma wannan fa ba yana nufin cewa wata dama ce ta samun karin kudi ba ga manoman ba musamman kananan manoma na Afirka, wadanda daman noman nasu bai taka kara ya karya ba.
Kamar yadda Dr Kulkarni ya nuna fatara da talauci na karuwa, abin takaicin ma kuma farashi shi ma na karuwa, wanda hakan na bata duk wani kasafi da suka yi.
A karshe dai tashin farashin kayan abinci na jefa al’umma cikin fatara da talauci da matsaloli na rashin lafiya da rashin cigaba.
Me za a iya yi?

Yayin da a kasashen da suka ci gaba mutane za su iya daukar wasu matakai masu sauki na iya fuskanta ko maganin matsalar tashin farashin abinci, inda wasu za su iya rage sayen wasu abubuwa ko rayuwa mai tsada, da rage tafiya hutu wata kasa, ko ma dai su rage kasafinsu na gida, a kasashe masu tasowa ko na masu karamin karfi, abin ba haka yake ba, domin daman su a kure suke ganin yadda ta kai ga mata na mika kansu ga maza da za su yi jima’i da su domin su ba su abinci.
Domin shawo kan wannan matsala hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, na yankuna da gwamnatocin kasashe ka iya daukar wasu matakai na al’ada wato da aka saba da su domin ceto jama’a daga fatara, kuma kungiyoyin agaji da yawa na mayar da hankali kan wasu dabaru domin tallafawa.
Babban jami’in shirin abinci da aikin gona na Majalisar Dinkin Duniya, Qu Dongyu, ya ce tallafa wa ayyukan noma na samar da abinci da bayar da taimako na tsawon lokaci suna daga cikin matakan fitar da jama’a daga matsalar. Ya kara da cewa yanzu ya kamata a tashi a tunkari matsalar babu sauran lokaci da za a bata.
Amma kuma Collacott ya gaya wa BBC cewa ba za a iya magance matsalar karanci ko fatarar abinci da kudi ba kada, ya ce akwai bukatar daukar tsauraran matakai domin a sauya tsari da abubuwan da suke jefa mutane cikin fatara.
Duniya baki daya kowa ya tashi tsaye, gwamnatoci da hukumomi da kamfanoni dda kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka damu da talakawa su sauya tsarin da ake ciki, su kirkiro tsarin da ke barin mutane a baya.
Gidan rediyon manoma (Farm Radio International), wanda cibiya ce ko kungiya mai zaman kanta ta bayar da tallafi da ke kasar Kanada, tana amfani da tattaunawa ta rediyo wajen wayar wa da kananan manoman kasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara kai da amsa musu tambayoyinsu.
Me za a yi yanzu?

Yayin da mutane a fadin duniya a manya da kananan kasashe kila ke tunanin yadda za su fuskanci matsalar tashin farashin kayan abinci, masu fafuta suna da karfin gwiwa cewa za a iya maganin tabarbarewar lamarin idan har shugabannin duniya za su dauki matakan gaggawa kuma wdanda suka dace.
Suna ganin ya kamata a bayar da dama mata da maza da matasa manoma su fadi abubuwan da suke damunsu, a rika tsare-tsare da su , a tallafa musu, ta hanyoyi daban-daban. Dr Kulkarni ita ma na ganin ta irin wanan hanya za a iya magance matsalar da ake ciki, to amma kuma ta yi gargadin cewa muddin aka kawar da kai to fa al’amura ba za su yi kyau ba a gaba.
-Source:BBCHausa-