Raiola zai tattauna da Man City kan Haaland, Sterling na son sanin makomarsa

Ana sa ran agent ɗin Erling Braut Haaland wato Mino Raiola zai tattauna da Manchester City a watan Janairu kan batun yiwuwar komawar ɗan wasan gaban na Dortmund da Norway mai shekara 21 a kaka mai zuwa.

Ɗan wasan gaban Ingila, Raheem Sterling mai shekara 21 na son tabbaci kan cewa yana cikin tsarin Pep Guardiola kafin ya soma shirin tattaunawa kan batun kwantiraginsa da Manchester City. (Sun)

Liverpool na son sayar da ɗan wasan tsakiyar Ingila Alex Oxlade-Chamberlain mai shekara 28, amma sai dai ga wanda kudinsa suka kai – a yanzu dai tsohon kulob ɗinsa Arsenal na son ya dawo. (Mirror)

Su ma Liverpool sun soma tattaunawa kan batun sayen ɗan wasan gaban Barcelona da Faransa Ousmane Dembele mai shekara 24, inda ake sa ran zai tafi a kyauta a kaka mai zuwa. (Mail, via Mundo Deportivo)


Phil Foden

Ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 21 Phil Foden na daf da sa hannu kan sabuwar kwantiragi da Manchester City. Kwantiragin da yake da ita a halin yanzu za ta ƙare ne a 2024. (The Athletic, subscription required)

Manchester United ta shiga layin su Chelsea da Juventus a neman da suke yi wa ɗan wasan tsakiyar Faransa da Monaco wato Aurelien Tchouameni mai shekara 21. (Express)

Yan wasan Southampton na jiran a kori kocin kulob ɗin Ralph Hasenhuttl mai shekara 54 a makonni masu zuwa inda har yanzu kulob ɗin bai samu nasarar cin wani wasa a gasar Premier ba. (Football Insider)

Ɗan wasan bayan Jamus, Antonio Rudiger mai shekara 28 zai yi shawara kafin ya yanke shawara kan makomarsa a Chelsea ganin cewa kwantiraginsa za ta ƙare a ƙarshen kaka. (Sky Sports)


Sam Johnstone

Southampton da Tottenham da West Ham na son sayen golan West Brom da Ingila Sam Johnstone mai shekara 28. (Hampshire Live)

Ɗan wasan bayan Sifaniya Hector Bellerin mai shekara 26 ya yi ƙarin haske kan cewa ba shi da niyyar komawa Arsenal idan ya gama zaman aro da yake yi a Real Betis. (El Desmarque, via Mail)

Leeds United na daf da sayen ɗan wasan Sifaniya mai shekara 17 Mateo Joseph Fernandez. Leeds sun yi tayin fam 450,000 sai dai Espanyol na san fam miliyan 1. (Team Talk)

Real Madrid ta ƙagara ta dawo da ɗan wasan Tottenham Sergio Reguilon mai shekara 24 a zaman aron da yake yi kafin kaka mai zuwa. (Defensa Central, via Express)

-Source: BBCHausa-

2 thoughts on “Raiola zai tattauna da Man City kan Haaland, Sterling na son sanin makomarsa

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.