Rabuwar Kawuna A Tsakanin Shugabannin APC Na Tarnaki Ga Zaben Fidda Gwani

An samu rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC da hakan ya kawo tarnaki ga zaben fidda gwani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

ABUJA, NIGERIA — Yayin da shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ke cewa Sanata Ahmad Lawan ne gwanin da a ka canka, sauran shugabannin jam’iyyar na cewa ba da su a ka dau matsayar ba.

Wannan dambarwa ta kai ga gwamnonin arewa na APC su ka gana da shugaba Buhari wanda ya ce sam bai canki wani daga ‘yan takarar ba, don haka a tafi a gudanar da zabe.

Gwamnonin dai da su ka ce sun zabi tikitin jam’iyyar ya koma kudu sun samu mara baya daga akasarin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Za a jira a talatar nan a ga wanda zai zama gwanin na APC wanda zai iya zama wa imma na gwamnoni ko kuma na masu fadi tashin wanzuwa a madafun iko.

– Source: VOAHausa –

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.