NIJER: Matsalar Tsaro Ke Ta Addabarmu- Bazoum Mohamed

Shugaban kasar Nijer, Mohamed Bazoum ya bayyana cewa, babban abin da ke gaban gwamnatinsa shi ne batun shawo kan matsalar tsaro.

WASHINGTON DC —  Shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata hira da shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sokoto yayin ziyarar aiki da ya je a kasar.

A hirar ta su shugaban kasar Mohamed Bazoum ya tabo mahimman batutuwa da dama da suka shafi kalubalen kasar, da ma kasashen waje.

Bazoum ya bayana cewar babban kalubalen da ya addabi kasar a yanzu shi ne na tsaro. Ya kuma kara da cewa yadda ‘yan ta’adda suka canza salo, suna karbe wa talakawa dabbobi, sannan kuma kwace kudinsu da sunnan haraji ko kuma zakkah abu ne mai matukar tada hankali.

-Source: VOAHausa-

One thought on “NIJER: Matsalar Tsaro Ke Ta Addabarmu- Bazoum Mohamed

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.