NIJAR: An Yi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 100 A Harin Hadin Guiwa

Hadin guiwar sojojin jamhuriyar Nijar da takwarorinsu na Burkina Faso sun yi nasarar wargaza wani sansanin ‘yan ta’adda dake kan iyakar kasashen biyu, lamarin da ya ba su damar kashe ‘yan ta’adda kusan 100 tare da kama makamai da babura fiye da 200.

WASHINGTON — A yayin rawar dajin da aka yiwa lakabin Taanli 2 dake nufin kawance a harshen Gourmantchi ne hadin guiwar dakarun Nijar da na Burkina Faso ya gudanar da wannan babban aikin kakkaba akan iyakokin kasashen biyu daga ranar 25 na watan November zuwa jiya Alhamis 9 ga watan Disamba.

Hakan ya bada damar samun nasarori kamar yadda Ministan tsaron kasar Nijar Alkassoum Indatou ya bayyana lokacin da shi da takwaransa na Burkina Faso suka ziyarci askarawan kasashen 2 a barikin sojan DjaDja dake garin Tilabery.

Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Yace a sansani 1 tak na ‘yan ta’ada sun yi nasarar lalata babura fiye da 250 sai a kyasta yawan mutanen dake amfani da wadanan babura 250. Ya kara da cewa, sun kuma sami lita sama da 2000 na sinadarin asid wanda ‘yan ta’adda ke amfani da shi don hada boma boman gargajiya. Haka kuma a sansani 1 kawai sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 80 idan aka yi jimillra gawawakin fiye da 100 ne aka bizne.

Ministan tsaron kasar Burkina Faso General Aime Barthelemi Simpore ya ce sun sami kyawawan sakamako ta hanyar wannan samame kuma hakan na nuna irin wannan aiki na hadin guiwa shi ne ya dace da yaki da irin barazanar da ake fuskanta a yau, wato a hada karfi wuri 1 domin gudanar da aikin hadin guiwa don samun nasara.

Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Da yake fashin baki akan wadannan nasarori na dakarun kasashen Nijar da Burkina Faso, masani akan sha’anin tsaro Abdourhamane Alkassoum yace aiki ya yi kyau amma kuma akwai bukatar daukan wasu mahimman matakai.

A wani labarin na daban jami’an tsaron Nijar da hadin guiwar takwarorinsu na Najeriya sun yi nasarar kama harsasai fiye da 1000 hade da wasu makamai da milioyon Naira da makudan kudaden cfa a hannun wasu ‘yan bindiga akan iyakar Maradi da jihar Katsina a ranar laraba da ta gabata.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.