‘Ni bakar fata ce, abokin zamana farar fata ne – ku daina tambaya ta ko wannan jaririyata ce’

'I'm black, my friend is white - stop asking me if this is my baby'

Lokacin da Ena Miller ta haifi jaririyarta a shekarar da ta gabata, ba ta shirya jin maganganu marasa dadi game da kamannin ‘yarta ba.

Tun daga ranar da na haifi jaririyata aka fara surutai da gulma game da launin fatarta, in ji ta.

“Bayan shafe kwana daya da wuni a sashen lura da masu cuta mai tsanani, Bonnie ta sake haduwa da ni na sa’oi kadan kacal, a daidai lokacin da wata mata ta leko daga bakin kofa ta tambaye ni abin da nake bukata na yi karin kumallo da shi.

Kafin na ba ta amsa, ta tambaye ni, ‘Waccan jaririyarki ce?’

Na yi tsammanin abin da za ta sake fada na yabawa ne – “Tana da kyau” ko “Kumatunta sun yi bulbul!”

A maimakon haka ta sake maimaita, “Shin da gaske jaririyarki ce?”

Yanayin maganarta cikin ban mamaki, da kuma ‘yar kaduwa. Kalmar da ta yi amfani da ita “da gaske” ta kara nuna akwai damuwa.

“Fara ce ita. Kalli gashinta, a mike yake. Fara ce sosai,” a cewar ta.

Daga haka duka komai ya fara – mutane na fitowa gaba-gadi su tambaye ni ko ni mahaifiyar Bonnie ce, ko kuma su rika magana a kan launin fatarta.

Ya fara a asibitin da na haihu. Zai ci gaba da faruwa nan gaba idan na fita sayayya, ko zama a gidan cin abinci da kuma ziyartar kawaye.

Ni bakar fata ce. Abokin zamana farar fata ne. Bonnie ruwa biyu ce.

Daga sashen kula da masu haihuwa na aike wa da mutanen da nake kauna hotunan Bonnie kuma kadan ne suka rubuta kalamai cikin layi daya, ba masu dadi ba kamar yadda duk wata mai jego za ta yi tsammani.

“Fara ce sosai.”

“Na fi son hoton da ta fi kama da ‘yar Afirka.”

“A koɗe take sosai, ko ba haka ba?”

Wani ma ya yi amfani da manyan baki : “Ita fara ce har yanzu.”

Mun shafe kwanaki biyar a asibiti ni da Bonnie kadai. Lokacin sabuwar barkewar korona ne – ba a amince wa baki zuwa ba.

Abokin zaman a kan duba mu ne kawai ta bidiyo a cikin manahajar WhatsApp wanda hakan na nufin inda da lokacin bincika shafin matambayi bay a bat ana Google tare da shiga damuwa game da maganganun mutane.

Shin mutane za su ci gaba da tunanin cewa ni ba mahaifiyar Bonnie ba ce?

Shin a koda yaushe Bonnie za ta kasance a bayana ko ni wacece?

Shin za a koda yaushe za a rika zato mai reno ce?

Ban shirya kasancewa ckin wannan hali ba.

Makonni biyar bayan sallamar mu daga asibiti, tafiyar da nake yi cikin jin dadi da juye ta zama damuwa. Wani mutum ya bayyana, yana yi min ihu,” Me ya sa jaririyarki ta zama fara sosai?” Ya rika kewaya mu, cikin bacin rai.

“Me ya sa ta yi fari sosai? Kin yi mu’amala da wani farar fata ne? Abinda kan faru kenan idan ka yi mu’amala ta farar fata! Kalle ta, kalle ta, kalle ta – me ya sa ta yi fari sosai?”

Na kadu, na tsorata, kana na ji kunya kan yadda ya tara min jama’a. Na kasa gane dalilan da suka saka wannan mutumin, wanda launin fatarmu iri daya ne, ya nuna bacin rai haka.

A gaskiya, duka kalamai marasa dadi game da launin fatar jaririyata daga mutanen da muke da tushe iri daya ne. Na kasa ganewa. Ban taba tsammani iyalai ruwa biyu kan shiga irin wannan hali ba.

Babban abin da na ke nadama a kai shi ne ban kare iyalai na ba. Ban ce komai ba. Na yi tafiya ta na bar wurin wannan mutum, idanuna cike da kwalla har na isa gidana. Ban taba magana kan tasirin da hakan ya yi min ba – har sai da na hadu da Wendy.

Short presentational grey line

Shekarun Wendy Lopez 60, tana zaune a yankin Kudancin London kuma ta yi kokarin ganin cewa duk wasu abubuwan rayuwa ba su dame ta ba.

Shekaru ashirin da takwas da suka gabata ta haifi Olivia. Kawarta ta kira sashen lura da masu haihuwa daga Guyana a Amurka ta Kudu don jin ko jaririyarta farar fata ce ko baka. Wendy ta yi dariya yayin da ta ke bayar da labarinta. Ta hakan ne ta rika magance abubuwa.

Olivia na da gashi mai launin ruwan makuba, amma daga gaba ”a kanannade yake”.

“Kai ka ce an kai ta wurin gyaran gashi ne kuma aka nannada mata abubuwan nannade gashi ne,” in ji Wendy

Wani likita ya tambayi Wendy ko cikin danginta akwai fararen fata, kuma ta bayyana cewa mahaifin Olivia farar fata ne. Amma ya ce: “a’a. a’a. a’a, akwai farar fata a cikin danginki shi ne dalilin da ya sa Olivia ta yi fari fat.”

“Ina tunani, ”Me yasa kake fada min duka wannan,” Wendy ta tuna. “Shin ya kan zagaya wurin duka masu haihuwar ya tattauna da su game da launin fatar jariransu? Ina mai tabbatar miki bay a haka.”

Wendy ta bayyana cewa mahaifiyarta ba ta amince da launin fatar jikarta ba, daga lokaci zuwa lokaci ta kan rika kiranta “baturiya” amma tana jin za ta iya daurewa da haka. Ya fi zama abin damuwa idan daga wasu mutane daban ne.

Akwai wani abin haushi da ya taba faruwa. Wendy ta fita sayayyarta ta mako-mako a Deptford, kudancin London tare da Olivia a cikin keken tura yara, a lokacin da ta wuce ta gaban wasu maza uku bakaken fata da ke tsaye a bakin wata mashaya.

“Daya daga cikinsu ya nufo ni. Ya kalli Olivia kana ya tambaye ni, ‘wannan ‘yarki ce?’

“Na ce masa a’a.’

“Na kawai nuna ba ‘ya ta ba ce, amma a cikin irin wannan halin na kan sake fadin haka.

“Ba na wata nadama. Na kan ji ana yi mini barazana. Na kan ji tsoro. Na ji lura a buge yake. Na yi tunanin zai iya dukan mu,” a cewar Wendy.

“Su a wurin su, ba daidai ba ne mace bakar fata ta kasance tare da maza fararen fata.”

Yanzu mutane su kan nuna rashin amincewarsu ta wasu hanyoyin, kuma Wendy ba ta yin shiru da bakinta – musamman ma saboda na da tawayar saurin koyon abu kuma ba za ta iya kare kan ta ba.

“Na je don a yi min allurar rigakafin korona a watanni kadan da suka gabata, kuma ma’aikaciyar jinyar ta tambayeni shin ko ni mai renon Olivia ce, kuma da na ce ni mahaifiyarta ce, ta sake tambayata ko shin ni ce ainihin wacce ta haife ta,” in ji Wendy.

“Ba zan rika kyale mutane na fada min abinda suka ga dama ba.”

Ta bayyana cewa yana da muhimmanci saboda kalamai irin wadannan nuna batanci ne game da asalin Olivia, kuma idan da ‘yarta za ta iya, za ta zagaya ko ina tana fada wa mutane su kyale ta: ”Mahifina farar fata, mahaifiyata bakar fata kuma ku kyale ni a haka.”

Na fada wa Wendy wani abu da ya dade yana ci min tuwo a kwarya. Shin mu – ko kuma ni din – na cika damuwa da yawa ne?

“Aammm..toh, ta ce,” tana murtsuka hannayenta biyu,” abin da wadanda ba su samu kan su cikin wannan hali za su ce kenan: ‘Oh kin cike damuwa. Haba, ba ma nufin wani abu a kan haka. Kina da Oh, kin cika saka damuwa a ran ki.'”

Amma bayan watanni 14 a kan haka, na gaji da yawan bayanai na tabbatar wa mutane cewa wannan kyakkyawar halittar da nake dauke da ita diyata ce.

Short presentational grey line

“Muna cikin Karni na 21. Za ka rika tunani mutane kan su yaw aye, amma ba haka ba ne,” in ji Fariba Soetan, wacce ta yi rubuce-rubuce a shafin intanet kan haihuwa da kuma girmar da yaran da suke ruwa-biyu.

Shekarun Fariba 41, kuma rabinta ‘yar kasar Iran ce, rabin Baturiya. Mijinta dan Najeriya ne, kuma ‘yayansu mata uku, masu shekaru 10, da takwas da kuma shida.

“Na tsorata da irin maganganu da ken una adawa da haihuwar ‘yaya mata uku da duka suke da launukan fata daban-daban,” in ji Fariba. “Na rig ana fahimci abubuwan da ‘yayana za su fuskanta game da yadda ake kallon su a cikin al’umma.”

Akwai abu daya da ya bata mata rai a shekarar da ta gabata. Fariba ta je daukar ‘yarta mai shekaru bakwai daga makaranta a Arewacin London.

“Na rungume ta, sai daya daga cikin yaran ta ce,”’Yar k ice wannan?’

“Na ce, ‘Eee’. Sai ta ce,’ Kuma kina son ta duk da cewa tana da irin wannan launin fata?’

“‘Ya ta ta ji wannan,” Fariba ta ce, a yayin da ta ke kokarin hana kan ta yin kuka.

Amma rubutu kan wannan batu ya taimaka. ” Ya sa na rika jin karfin gwuiwa. Ba wai kawai ina yi ba ne, amma ina yin wani abu game da haka.”

Na so Fariba ta b ani tabbacin cewa wannan wani bangare ne kawi kuma mutane za su daina yin katsalandan din da bai dace ba. Amma abin takaici, bata yi hakan ba.

“Akwai yawan surutai bayan da muka tafi hutu, musamman a kan babbar ‘yata, wacce ta fi su duhu,” in ji Fariba.

“‘Oh… ta yi ‘nunar rana ne’ ko ” Ta yi baki sosai.” Akwai kuma wasu yanayin kalamai na, ” Kina so ki kasance mai irin wannan launin fata?’

“Ta kan jure wasu daga cikin su. Ba ta son ta yi baki sosai saboda akwai abubuwa marasa dadi da ake dangantawa ta shi.”

Sai kuma Asha, wacce muke magana a kai. Ta dawo daga wurin motsa jiki cike da kuzari da karfi. Tana so ta nuna min littafan da ta fi so, tana son ta nuna min nadadden gashinta da kuma kasancewa tauraruwar rawar ballerina.

“Wasu lokuta na kan kalli mutane a kan titi kuma na kan yi mamaki idan daga zuriya daya muka fito,” in ji Asha.

Ta bullo da nata hanyoyin warware matsalar.

“Ina danganta iyalai ko wanne da dandanon ice-cream. Ni dandanon caramel ce. Mahifiyata kuma ‘vanilla’ ce. Mahaifina kuma cakulet. Ella ita kuma kana kuma ‘fudge’, sannan kanwata ‘butterscotch’.

“Ya fi kyau idan kana tunanin su ta wannan hanyar – a maimakon cewa kai ka fi haske, ko kai ka fi ni baki, don haka ba ma raba tsakaninmu.

“Ina so in kwatanta mu ta hanyar amfani da abubuwa masu dandanon dadi. Abubuwan da mutane ke kauna – kamar ice cream. Mu iyalai ne don haka kada ka rika yi mana miyagun kalamai.”

Lokacin da ta ke rawa yayin da ta ke kokarin komawa cikin gidansu, Fariba na cike da fatan mutane irin su Meghan Markle da kuma mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris za su karfafa gwuiwar mutane su sauya tunani game da launin fata – ko da ya zama wanda zai iya neman sanin asalinsa na kasancewa bakar fata, ko kuma tunanin mutane na lokacin mulkin mallaka na cewa fari ya fi kyau.

“Ina fatan ganin cewa wani abu na sauyawa. Ina gay a kamata mu cigaba da wannan fata.”

A cikin watanni 14, gashin kan Bonnie ya nannade, kana launin fatarta ya sauya.

Bayan makonni kadan na hadu da Wendy, ta aike min da sakon kar-ta-kwana don jin ina aka kwana game da tattaunawarmu.

“Ina fata komai na tafiya daidai,” ta rubuta. ”Na manta in ce: ki kasance cikin farinciki tare da ‘yarki, saboda wadannan shekaru masu albarka za su wuce.”

Shawara ce da nake farin cikin dauka.

A shekarar 1980 ne aka bayar da wata jaririya riko saboda kasancewa mai launin fatar da bata dace ba – ruwa-biyu ce ita, iyayenta fararen fata ne, kuma wannan nuna wariyar launin fatar Afirka Ta Kudu ne. Amma kasancewa ma’aurata turawa ne suka rene ta a Birtaniya ya sa ta fara neman tushenta a duniya. Ta gano ne bayan da ta sake dawowa kasarta ta haihuwa

-Source: BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.