Newcastle na son Coutinho da Werner, Madrid na son Rudiger

Waɗanda suka mallaki ƙungiyar Newcastle ƴan Saudiyya na shirin fara sa ido kan irin nasarorin Jurgen Klopp da Thomas Tuchel a Ingila.

Dan wasan gaban Chelsea da Jamus mai shekara 25 Timo Werner na daga cikin manyan yan wasan da kulob ɗin ke hari da kuma ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Niklas Sule mai shekara 26 da ɗan wasan Barcelona da Brazil mai shekara 29 Philippe Coutinho da kuma tsohon ɗan wasan Jamus Lucien Favre. (Bild – in German)

Newcastle ɗin ta tuntuɓi wakilan ɗan wasan bayan Leicester da Faransa Wesley Fofana kan batun komawarsa kulob ɗin a watan Janairu. (RMC Sport – in French)

Ɗan wasan tsakiyar Juventus da Faransa Adrien Rabiot na daga cikin waɗanda aka alaƙanta da Newcastle ɗin, inda Juventus ɗin ke son sayar da ɗan wasan mai shekara 26 a watan Janairu domin samun kuɗin da za ta sayi ɗan wasan Monaco Aurelien Tchouameni ko kuma ɗan wasan tsakiyar Manchester United Donny van de Beek mai shekara 24. (Calciomercato – in Italian)

Monaco ta yi wa ɗan wasanta Tchouameni mai shekara 21 kuɗi kan euro miliyan 60, inda Real Madrid da Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool duk ke rububin ɗan wasan. (Marca – in Spanish)

Barcelona na son sayar da Coutinho a watan Janairu inda Liverpool ke son ta dawo da shi Merseyside. (El Chiringuito TV, via Express)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers na daga cikin waɗanda Newcastle ke neman idan sabbin masu kulob din suka yanke shawarar korar Steve Bruce. (Sky Italy via Mirror)

Sai dai an bayyana cewa Rodgers ɗin ya fi son ya ci gaba da zama a kulob ɗin da yake jagoranta. (Telegraph)

Antonio Rudiger

Real Madrid na son sayen ɗan wasan bayan Chelsea Antonio Rudiger mai shekara 28. Kwantiragin ɗan wasan za ta ƙare a ƙarshen kakar nan. (Marca in Spanish)

Phil Foden na da tabbacin zai saka hannu a sabuwar yarjejeniya da Manchester City ta kusan fam miliyan 50 inda ɗan wasan mai shekara 21 na Ingila zai samu kusan fam 150,000 a duk mako. (Mirror)

Arsenal na shirin fara cinikin ɗan wasan Club Bruges mai shekara 22 Noa Lang inda za ta fara tayinsa daga euro miliyan 30.

-Source: BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.