Mutum da Takunkumi

Shimfida

Labarin zuciya….wai a tambaye fuska

Babu shakka a wasu lokuta da yawa fuskar mutum tana bayyana irin halin da yake ciki, ko na farin ciki, bakin ciki ko tausayi da sauran su.

Misali idan aka farantawa mutum zaka ga ya yi murmushi, ko yana cikin anashuwa, haka zalika idan aka bakantawa mutum sai kaga fuskar sa/ta ta turnuke.

Masana da yawa sun yi nazarce nazarce a kan muhimmancin yanayin fuska yake a wurin sadarwa, mu’mala da zamantakewa.

Yanayin fuskokin mutane na iya nuna   yadda suke ji a zuciya da nuna niyyar su a cikin yanayin zamantakewa.

Abubuwan da ke bayan fage wanda ake tsinkayar fuskoki suna ba da muhimman bayanai game da yanayin mutum ke ji a wannan lokaci.

Yanayin fuskoki yana da matukar muhimmanci kan yadda muke sadarwa da wurin habbaka dangantakar zamantakewar dake tsakanin mu.

Wannan makala ce akan tasirin da takunkumi ko kuma nosemask yake yi akan mutane,

amma na fara shimfida ta ne da yanayin fuska saboda yadda takunkumi ko kuma nosemask yake dashi a wurin sadarwa, mu’amala da zamantakewar mu.

Takunkumi

A ruwayar rumbun adana bayanan intanet na Wikipedia, takunkumi ko nosemask shine.

A shekara ta 1918 ce aka fara amfani da takunkumin yadi don kare yaduwar matsananciyar mura ta Spanish Flu a kasar Spaniya,

Sai dai a shekarun 1960 aka fara amfani da takunkumin zamani wanda likitoci da ma’aikatan asibiti ne suka fi amfani da shi, don kare shakar iskar kwayoyin cuttutuka daga marasa lafiya dake yawo a cikin iska, da kariya daga fantsamar miyau, majina ko gumin maras lafiya.

Tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19, ana cigaba da tafka mahawara akan amfani da takunkumin, inda wasu ke kafa hujja da yiwuwar karancin sa.

Sai dai tuni wasu kasashen duniya ciki har da Ghana suka kafa tare da tilasta bin dokar sanya takunkumi ko nosemask.

A cewar hukumar lafiya ta Duniya WHO:

Ya kamata ne a yi ta amfani da takunkumi nosemask a matsayin wani ɓangare na cikakkun dabarun matakan don kare yaduwar cutar da ceton rayuka; yin amfani da abin rufe fuska kadai bai isa ya samar da isasshen kariya daga kamuwa da cutar COVID-19.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Adoo a jawabin sa na baya baya akan cutar koro ya jaddada dokar kowa da kowa a kasar ya rinka sanya takunkumi a wani matakin dakile yaduwar cutar.

Don haka jami’an ‘yan sanda a Ghana za su iya kama ka idan baka sanye da takunkumi, musamman a taron jama’a.

A yau sama da kasashe hamsin (50) a duniya sun kafa dokar tilasta sanya takunkumi (nosemask)a wuraren taron jama’a, a wasu kasashen da babu dokar mutane suna sanya takunkumin don kare kamuwa da cutar ta korona.

Duk da cewar masana sun tabbatar da tasirin kariyar takunkumin nosemask, da yadda ‘yan sanda suke kama mutane amma wasu al’ummar Ghana zaka sun yi biris, wasu kuma sun bi dokar. Ga yadda tattaunawar mu ta kasance:

Takunkumi da Sadarwa.

Kamar yadda na fada tun farko, labarin zuciya a tambaye fuska, haka zalika ido shine tagar zuciya, kamar yadda baki yake yanka wuya, a lokuta da yawa daga kallon fuskar mutum zaka gan yanayin da yake ciki, misali idan ya fusata ne, ko yana cikin annashuwa, ko kuma tasowar sa kenan daga bacci.

Mafi yawancin mutane suna sanya takunkumin ne na nosemask don kare kai daga kamuwa da cutar korona amma shin yaya hakan yake tasiri a wurin mu’amalar mu da juna?

Gaba ɗaya, mutane su kan mayar da hankali a kan fuska baki daya maimakon mai da hankali kan abu daya, misali baki, hanci ko ido, in ji masanin halayyar ɗan adam Rebecca Brewer.

Wadda take nazarin rawar da yanayin fuska ke takawa a cikin hanyar da muke sadar da yadda muke ji a rai a Jami’ar Royal Holloway ta Landan. “Lokacin da ba za mu iya ganin fuska baki dayan ta ba, ana iya samun rikicewar sadarwa.”

Idan aka zo wurin nazarin yanayin da fuska take ciki, baki da ido sune suka fi bayar da bayani saboda yadda akafi amfani da su.

Muna nazari cikin natsuwa don fahimtar yadda motsin yankin baki da da’irar ido don fahimtar abinda mai magana yake fada, amma kowannen su yana iya bayyana yanayin da fuska take ciki.

Misali ana amfani da yankin baki wurin bayanna farin ciki, misali yin murmurshi ko dariya.

Amma dogaro da fuska ko wani yankin fuska wurin sanin yanayin da mutum yake ciki, a wasu lokutan yana da rikitarwa kamar yadda Aleix Martinez wani masanin latroni da komfuta na jami’ar Ohayo dake Amurka ya yi kashedi.

Aleix yana nazari ne a kan yanayin fuska ta yadda zai iya koyar da na’ura.

Ba dole ba ne sai mutum yana murna ko cikin wani farin ciki zai yi murmushi ko dariya ba, kuma ba kowanne lokaci ne mutumin da yake murna ko farin ciki yake murmushi ko dariya ba, inji masanin.

Hakika bincike ya tabbatar da akwai nau’in murmushi goma sha tara amma shidda ne kawai suke da alaka da murna ko farin ciki, sauran sha ukun suna alaka ne tsoro, kunya, mamaki da sauran su.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.