An tabbatar da mutuwar akalla mutane hudu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwahe kwanaki biyu ana a jihar Ashanti a Ghana.
Mutuwa na karshen ya rsata ne da wani wani mutum mai shekaru 70, mai suna Mr. Bernard Sarpong, wanda ruwan saman ya ja shi a unguwar Sokoban-Ampabame a cikin gundumar Atwima-Kwanwoma.
Sauran wadanda suka mutun sun hada ne da wani jinjiri mai shekara guda Awal Mohammed da Seidu Mohammed da kuma wata mace da hr Yanzu ba a iya ganota.
Da yake jawabi ga kamfnin dillnin labaran Ghana (GNA) a Kumasi, shugaban hukumar kai agaji lokacin bala’I a gundumar ta NADMO, Mr. Kwabena Nsenkyire, yace daruruwan mutane sun rasa matsugunan su.
Kadarori na dubban sidodin Ghana sun salwanta kana wasu ambaliyar ta lalatagine gine.
Unguwannin da da ambaliyar tafi barna sun hada ne daAbuakwa-Manhyia, Sawaba, Kejetia, Atafoa, Swua, Prabon, Atonsu, Santasi, Patasi, Danyame, Atasemanso da sauran su.
Shugban hukumr agaji a yankin Ashanti ya gargadi mutane da su tabbatar da matakan kare kan su da kadarorin su saboda masana yanayi sun yi kashedi za a kara samun ruwa kamar da bakin kwarya a cikin kwanaki masu zuwa.
Hukumar tana kokarin harhada kayan jin kai domin taimakawa mutane da bala’in ya rutsa da su.