Masu Ruwa Da Tsaki Sun Yi Hasashen Cewa Karin kudin Harajin Motocin Da Ake Shigo Da Su Zai Gurgunta Tattalin Arzikin Najeriya

La’akari da matakin kara kudaden haraji da gwamnati Najeriya ta yi kan motocin da ake shiga da su daga Kasashen waje, Kungiyar dillalan motoci a kasar da wasu masu tsokaci na cewa hakan na matukar haddasa koma baya ga fannin sufuri da kuma halin matsi da talaka ke fama shi a Najeriyar

Wasu masu ruwa da tsaki na gargadin cewa matakin rage yawan motocin da aka kera kasa da shekaru 12 zuwa 9 wadanda ake shigowa da su daga kasashen ketare zuwa Najeriya, na daga cikin abubuwan da suka kara tsananta haraji na shiga motoci kasar, ninkin tsohon farashin.

Shugaban kungiyar dillalan motoci a Najeriya, Injiniya Prince Ajibola Adedoyin, ya jaddada cewa wannan sabon tsari na taka muhimmiyar rawa wajen hauhawar farashin motoci a kasuwanni. Don haka sun tuntubi hukumar kwastam da ke da alhakin wannan aikin, don sama wa gwamnati kudaden shiga, amma ba su samu wani gamshasshen bayani ba.

Gwamnatin Najeriya dai ta sanya tsarin ne da nufin inganta samar da kudaden shiga a ksasar da kuma hanzarta yanayin da ake shigowa da kayayyaki cikin kasar

Sai dai a cewar wani masanin tattalin arzikin a Najriya, Yusha’u Aliyu, ya kamata gwamnati ta kara tasirin haka a wannan lokaci..

A nashi bangare, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Hassan Sardauna, cewa ya yi ya kamata gwamnati ta zauna tare da dillalan motoci don samun mafita da za ta amfani kowa.

Ko da yake dai gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa an yi wannan tsari ne don rage shigar da motocin da shekarun kerasu ya jima, sai dai kungiyar dillalan motocin sun bukaci gwamnati da ta sake nazari kan tsarin shekaru 12 na kera motocin da aka taba amfani da su zuwa shekaru 15…

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.