Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Kafa Hukumar Kula Da Bayanai Ta Kasa

Majalisar Dattawan Najeriya na shirin kafa wata hukuma da za ta rika kula da bayanai ta kasa, wadda za ta daidaita ayukan hukumomi da suka dace.

WASHINGTON DC — Dan majalisar dattawa mai wakiltan Taraba ta tsakiya kuma shugaban kwamitin kula da manyan ayuka na majalisar Yusuf Abubakar Yusuf ne ya gabatar da ita a gaban majalisar.

Dokar na da manufar taimakawa wajen kafa hukumar da za ta inganta kimar Najeriya a idon duniya ta hanyar kirkira da kiyayewa da sabunta bayanai da kidayar kamfanoni a Najeriya, da kuma samar da tsari mai inganci don daidaita ayukan hukumomi da suka shafi kasuwanci.

Yayin da yake bayani kan yadda hukumar za ta gudanar da aiyukan ta, Sanata Yusuf Abubakar ya ce duk bayanai da za su fito daga Gwamnati, ya kamata su zama bayanai sahihai.

Yusuf ya ba da misali cewa “idan aka nemi sanin yawan man fetur da ake hakkowa daga Najeriya, za a tambayi ma’aikatar man fetur ta kasa da ofishin kididdiga amma za’a iya samun alkaluma daban-daban, saboda haka wannan hukuma ita ce za ta daidaita bayanai na gaskiya da zai sa kasashen duniya irin su Amurka da Ingila da kasar China su amince ta bayanan.”

Shi kuwa daya daga cikin ‘yan kwamitin kuma Sanata Mai Wakiltan Kano ta Tsakiya Ibrahim Shekarau, ya ce tun shekara ta 2006 aka yi kidaya a Najeriya kuma kawo yanzu hasahe ake yi na yawan al’umma kasar.

“Wasu su ce miliya 200, wasu su ce 200 da ‘yan kai. To amma in akwai irin wannan hukuma, ita ce za ta tabbatar da yawan yan kasa sanan Ofishin kididdiga ya yi amfani da alkaluman wajen tsare-tsaren ayukan mahukunta” in ji Shekarau

Ya kara da cewa wannan babban aiki ne amma kuma mai sauki idan akwai hukumar.

To saidai ga mai fashin baki kan al’muran siyasa da gudanar da mulki Abubakar Aliyu Umar, wannan hukuma ba ita ce abin da ‘yan kasa ke bukata ba a halin yanzu saboda haka ba anan gizo ke saka ba.

Abubakar ya ce “al’umma na fama da talauci, yunwa da fatara, ga kuma masu sace mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa, an gagara magance matsalolin tsaro.”

Ya kara da cewa “mutane ba sa samun cin abinci sau uku a rana amma ‘yan majalisa suna dokokin da za su taimaka wa kan su da ‘ya’yansu ne kawai. Basira ta bacewa yan majalisar dokoki kaman ruwa ya kare wa dan kada ne bai gama wanka ba.”

An riga an yi wa kudurin dokar karatu na biyu har an bude dandalin sauraren ba’asin jama’a.

Idan an kafa Wannan hukuma, za ta samo kudaden ta na shiga da za ta gudanar da ayuka ta da kanta, ba tareda wani tallafi daga bangaren gwamnati ba.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.