Lafiya Zinariya: ‘Cutuka fiye da 200 ake dauka ta hanyar cin gurɓataccen abinci’

Cutuka fiye da 200 ne ake dauka ta hanyar cin abincin da ya gurbata da wasu kwayoyin cuta, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Haka kuma mutum daya cikin kowane goma ke kamuwa da rashin lafiya sakamakon cin gurbataccen abinci a duk shekara.

Hukumar ta bayyana wasu hanyoyin da abinci ke gurbata da suka hada da a lokacin da ake sarrafa shi ko dakonsa ko kuma a yayin da ake cinsa.

Sannan zai iya zama ta hanyar kasa ko muhallin da ya gurbata ko gurbatacce ruwa ko kuma gurbatacciyar iska.

Yadda aka adana abinci me na janyo gurbatarsa idan ba a adana shi yadda ya kamata ba, ko ba a sarrafa shi ta yadda ya dace ba.

WHO ta kara da cewa iri-iren cututtukan da ake dauka a abinci kan janyo larurori da suka kama daga gudawa zuwa kansa.

Sai dai mafiya yawansu sun fi shafar hanjin ciki, ko da yake wasu kan nuna alamomin kamar na kwakwalwa ko cututtukan da suka shafi mata, ko kuma cututtukan da suka shafi garkuwar jikin dan adam.

Hukumar ta bayyana cewa cututtukan da ke janyo gudawa sun kasance babbar matsala a baki daya kasashen duniya.

Amma girman matsalar ta ta’allaka da karfin kudin shiga, ko kasa na da karfin kudin shiga ko matsakaici ko kuma matalautan kasashe.

WHO ta ce kimanin mutane 420,000 ne ke mutuwa bayan cin gurbataccen abinci duk shekara a fadin duniya.

-Source:BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.