Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Sun Tantauna Matsalolin Matafiya A Yammacin Afrika

A jamhuriyar Nijer shugabanin kungiyoyin kwadago da na kungiyoyin fararen hula sun fara gudanar da taro domin nazarin hanyoyin magance matsalolin dake damun matafiya akan hanyoyin zirga zirgar kasashen Afrika ta yamma.

WASHINGTON DC — Duk kuwa da cewa gwamnatocin wadanan kasashe sun rattaba hannu akan yarjejeniyar kai da kawon jama’a da dukiyoyinsu ba tare da wata tsangwama ba a karkashin kungiyar CEDEAO.

Yawaitar koke koken jama’a a game da yadda jami’an tsaro ke tatsar kudade irin na ba gaira ba dalili akan hanyoyin zirga zirga musamman a iyakokin kasashen Afrika ta yamma ya sa kungiyoyin kwadago da kungiyoyin fararen hula shirya taro domin tantauna wannan batu dake kara kamari a kowace Safiya kamar yadda Mansour Adamou na kungiyar kwadago ta CDTN ya yi karin bayani.

Saukakawa al’umomi hanyoyin gudanar da harkoki a tsakanin kasashen yammacin Afrika na daga cikin manyan dalilai na ainahi da suka sa gwamantocin wannan yanki kafa kungiyar ECOWAS a matsayin wani matakin bunkasa tattalin arziki sai dai a zahiri ba haka abin yake ba a aikace.

Da yake bayyana tasa fahimta a dangane da yadda yake kallon abubuwan dake faruwa da matafiya a mafi yawancin kasashen CEDEAO Habibou Soumaila wanda ke halartar wannan taro da sunan kungiyar farar hula ta APAISE Niger na cewa ya kamata kasashen Afrika ta yamma su yi koyi da takwarorinsu na Turai.

A karshen wannan taro na tsawon wuni 2 mahalartan zasu bullo da shawarwarin da zasu gabatarwa gwamnatocin kasashen kungiyar ECOWAS ta yadda za a dauki matakan da suka dace da wannan matsala dake hanawa al’umomin yammacin Afrika morar ‘yancin zirga zirga yayinda a nan gaba hadin guiwar kungiyoyin kwadago da na farar hular ke saran kaddamar da ayyukan waye kan jama’a akan wannan maudu’i.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.