Muna Samun Nasara A Aikin Kidayar Mutane Da Gidaje-Agbeyen

Babban jami’in kididdiga a yankin arewacin Ghana dake aikin kidayar mutane da gidaje na wannan shekara, George Agbeyen ya bayyana gamsuwar shi game da yanda mutane suka basu hadin kai wurin gudanar da aikin su.

A cewar sa, yankin zai shiga cikin wurare da suka yi nasarar samun taimakon jama’a a aikin kidayar mutane da gidaje.

Shugaban na kwamitin aikin kidayar na yankin arewa, Alhaji Alhassan Isahaku ya yabawa jami’an ma’aikatar kidaddiga ta Ghana a kan irin rawar da suke takawa a wannan aikin kasa, yana mai cewa “koda yake aikin na daukar lokaci wani sa’ilin kuma yana da wahala,” amma kokarin su zai kai ga samun nasarar aikin kidayar mutane da gidaje na shekarar 2021.

Ya yabawa mambobin kwamitocin aikin kidayar daban daban a kan shawarwarin fasaha da na kwarewa da suke taimakawa da su wurin warware matsaloli da ake samu cikin aikin.

Alhaji Isahaku ya ce kowane mutum nada muhimmanci kana ya kamata a lissafa shi. Ya yi kira ga kafafen yada labarai da su ci gaba da taimakawa aikin kidayar a yankin ya yi nasara fiye da duk yankunan kasar.

A halin da ake ciki kuma, a nasa bangare, ministan yakin acrewacin kasar, Alhaji Alhassan Shani Shaibu ya ce tattara bayanai yana da muhimmanci ga ci gaban kasa, yana mai cewa gane shekarun al’umma da kungiyoyin su da addinan su da kabilun su da sauran yana da mihimmanci ga masu tsara harkokin kasa ta yanda zasu shiryawa kasar ci gaba.

Alhaji Shani ya yi kira ga jami’ai da su kula sosai wurin gudanar da aikin, yana mai cewa cin nasarar aikin baki daya ya ta’allka ne a kan su.

Ya kuma yi kira ga jami’an da su tattarawa Ghana bayanai mafi inganci domin tabbatar da ci gaban kasar.

Sama da ma’aikatan kidaya 5,392 da masu sa ido ne aka dauka a yankin arewacin Ghana domin gudanar kidayar mutane a wannan shekara, an dauki jumular jami’an sa ido dake yawo a gundumomi su 39 kana da manyan jami’an kididdiga na matsayin gunduma 17 suke aikin.

-Source: Myjoyonline-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.