Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Mbappe, Pogba, Locatelli, Simy, Ward-Prowse, Bowen, Dumfries

Real Madrid za ta fara tattaunawa da Paris St-Germain a makonnin da ke tafe domin sayen dan wasan gaba na tawagar Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara ta gaba. (90min)

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba, mai shekara 28, wanda ake ta danganta shi da tafiya Paris St-Germain, na iya ci gaba da zaman a tsawon lokaci a Old Trafford, amma kuma watakila dan kasar Faransar ba zai kulla yarjejeniyar tsawaita zamansa da Red Devils din a bazaran nan ba. (Sky Sports)

Pogba ya jima yana son barin Manchester United

Har yanzu kociyan Liverpool Jurgen Klopp yana da burin dauko dan wasan tsakiya na Borussia Monchengladbach Florian Neuhaus, mai shekara 24, amma kuma ba lalle ba ne Reds din su iya sayen dan wasan na Jamus a farashin da kungiyarsa ta yi masa na fam miliyan 34 . (Sport1 – in German)

Liverpool ta bi layin Juventus da Arsenal a fafutukar sayen dan wasan tsakiya na Italiya da suka ci kofin kasashen Turai na Euro 2020 Manuel Locatelli, mai shekara 23, daga Sassuolo. (Gazzetta dello Sport, daga Mail)

Ana danganta Manuel Locatelli da nasarar da Italiya ta yi ta cin kofin Turai

Kungiyar Chelsea a shirye take ta rage farashin da ta sanya wa dan wasanta Tammy Abraham mai shekara 23, fam miliyan 40. Dan wasan na Ingila wanda Arsenal da West Ham da kuma Aston Villa suke so. (Sun)

Manyan kafofi a Liverpool ba sa musanta rahotannin da ke alkanta dan wasan gaba na West Ham, dan Ingila Jarrod Bowen mai shekara 24. (Star)

Arsenal a shirye take ta ba wad an wasanta na tsakiya Granit Xhaka, mai shekara 28, sabon kwantiragi, bayan da rahotanni ke danganta dan wasan na tawagar Switzerland da tafiya Roma. (Athletic)

Arsenal ta yi watsi da tayin fam miliyan 12.9 da Roma ta yi wa Xhaka

Tottenham na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba dan Najeriya Simeon Tochukwu Nwankwo, wanda ake kira Simy mai shekara 29, wanda ya ci wa Crotone da ta fadi daga gasar Italiya ta Serie A, kwallo 20. (Telegraph)

Southampton ta ki yarda da tayin fam miliyan 25 da Aston Villa ta yi wad an wasanta na tsakiya, dan Ingila James Ward-Prowse, mai shekara 26. (Athletic)

Newcastle United na shirin sabunta kwantiragin kociyanta Steve Bruce, mai shekara 60,da wata shekara uku. (Star)

Nwankwo ne dan wasan Afirka da ya fi ci wa Crotone kwallo a Serie A

Har yanzu Everton ba ta yanke shawara ba a kan dan bayan PSV Eindhoven Denzel Dumfries mai shekara 25, duk da cewa darektan kwallon kafa na kungiyar ta Premier Marcel Brands na sha’awar dan wasan na Holland kuma ana tattaunawa da kociyanta Rafa Benitez a kansa. (Liverpool Echo)

Leeds United na tattaunawar farko-farko a kan sayen dan wasan tsakiya na Huddersfield Town, dan Ingila Lewis O’Brien mai shekara 22. (Football Insider)

Wasu rahotanni na cewa Crystal Palace da Brentford da kuma Watford na sha’awar sayen dan wasan tsakiya dan kasar New Zealand Matthew Garbett, mai shekara 19, wanda ke taka wa kungiyar Falkenbergs ta Sweden leda. (Sun)

-Source: BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.