Ana sa ran Newcastle za ta nemi tsohon ɗan wasan tsakiyan Liverpool Philippe Coutinho inda ake ganin Barcelona ta ƙagara ta rabu da ɗan wasan na Brazil mai shekara 29. (Sport)
Manchester United na shirin fara neman ɗan wasan tsakiyan Monaco kuma ɗan ƙasar Faransa Aurelien Tchouameni mai shekara 21 a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin ɗan wasan Faransar nan mai shekara 28 Paul Pogba. (Football)
Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe ya buƙaci a saka batun gasar Olympics a duk wata yarjejeniya da zai saka wa hannu da Real Madrid bayan ɗan wasan mai shekara 22 ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta wakiltar Faransa a wasan Olympics da za a buga a Paris a 2024.
Ƙungiyar Palmeiras ta Brazil na son sayen ɗan wasan gaban Manchester United Edinson Cavani mai shekara 34 idan kwantiragin ɗan wasan na Uruguay ya ƙare a kaka mai zuwa. (Daily Express)

Kocin Villarreal Unai Emery mai shekara 50 ya fasa komawa Newcastle sakamakon kulob din na so ya saka wani sakin layi a kwantiraginsa da zai ba Newcastle ɗin damar korarsa muddin ta zama kashin baya ƙarshen kaka. (Daily Mirror)
Manchester City ta shaida wa kocin Leicester Brendan Rodgers mai shekara 48 cewa za ta buƙace shi idan Pep Guardiola mai shekara 50 ya bar kulob ɗin. (The Transfer Podcast via Leicester Mercury)
Tottenham ce kan gaba wajen neman ɗan wasan gaban Fiorentina mai shekara 21 Dusan Vlahovic inda ɗan wasan na Serbia a shirye yake ya koma kulob ɗin da ke buga gasar Premier. (La Nazione – in Italian)

Barcelona na sa ran zaunar da Ousmane Dembele mai shekara 24 domin ɗan wasan na Faransa ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ta shekara uku a ƙarshen Nuwamba. Dembele wanda kwantiraginsa zai ƙare a kaka mai zuwa , ana raɗe-raɗin cewa ya amince da rage masa albashi. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Everton na tunanin neman ɗan wasan tsakiyan Real Mallorca da Ghana Iddrisu Baba mai shekara 25 a watan Janairu. (Fichajes via Daily Mail)
Wolves na son ta gaggauta tattaunawa da RB Leipzig domin mayar da aron da aka bayar da dan wasan gaban Koriya Ta Kudu Hwang Hee-chan zuwa yarjejeniya ta din-din-din. Akwai yiwuwar
Barcelona za ta nemi ɗan wasan tsakiyan Tottenham mai shekara 24 Tangu Ndombele a watan Janairu, sai dai aro kawai ake ganin za ta iya ɗaukar ɗan wasan na Faransa. (Sport – in Spanish).
-Source:BBCNews-