Kasar Mali Ta Ce Zata Fice Daga Rundunar G-Sahel

Ranar Lahadi gwamnatin kasar Mali ta fadi cewa zata fice daga rundunar dakarun kasashen yammacin Afirka da ke yaki da ‘yan ta’adda don nuna rashin jin dadinta da kin amincewa da ita a matsayin shugabar kungiyar ta G5-Sahel ta yankin, wacce ta hada da Mauritania, Chadi, Burkina da Nijar.

Washington, DC – A wata sanarwar gwamnatin Mali, ta ce gwamnati ta yanke shawarar janyewa daga dukkan sassan kungiyar G5-Sahel, ciki har da rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ‘yan ta’adda.

An kafa kungiyar G5 Sahel ne a shekarar 2014 kuma a shekarar 2017 ta kaddamar da yaki da ‘yan ta’addan.

Tun a watan Fabarairun shekarar 2022, aka shirya yin wani taron shugabannin kasashen G5-Sahel a Bamako don kaddamar da Mali a matsayin kasar da zata shugabanci kungiyar.

Amma kusan watanni hudu bayan wa’adin, da alama “har yanzu ba a yi taron ba,” a cewar sanarwar.

Gwamnatin Mali ta ce adawar da wasu kasashe mambobin kungiyar G5-Sahel ke yi game da shugabancin Mali a kungiyar na da alaka da yunkurin wata kasa da ke wajen yankin da ke neman mayar da Mali saniyar ware, ba tare da bayyana sunan kasar ba.

Tun a ranar 9 ga watan Janairu ne dai kasar Mali ke fama da takunkumin karya tattalin arziki da diflomasiyya da kasashen yammacin Afirka suka sanya mata don ladabtar da gwamnatin sojan kasar saboda matakin ci gaba da mulkin kasar tsawon wasu shekaru, biyo bayan juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2020 da Mayun 2021.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.