Karancin Wutar Lantarki Ya Tilasta Wasu Jihohin Najeriya Kai Gawarwakinsu Kasar Nijer

A Najeriya karancin samun wutar lantarki  na tilasta wasu asibitoci na Jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar tura gawarwakin zuwa kasar domin kar su lalace saboda rashin sanyi a wuraren ajiye su.

WASHINGTON — 

Wannan na zuwa ne lokacin da al’ummomi ke nasarar samun tallafin ababen more rayuwa domin samun saukin rayuwa.

Salwantar rayukan jama’a a Najeriya abu ne da ya zamo ruwan dare domin kusan ba safiyar da ba a samun rahoton salwantar rayuwa.

Sau tari ana ajiye gawa a asibitin ne kafin a mika ta ga iyalan mamacin sai dai wasu asibitoci kamar na garin Illela a Sakkwato da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar. Matsalar wutar lantarki t kan sa wani lokaci ba a barin gawa ta kwana a yankin.

Hakan ne yasa dan majalisar tarayya mai wakiltar Illela da Gwadabawa, Abdullahi Balarabe Salame ya samar da manyan injunan wutar lantarki 3 domin rage wannan matsalar.

Har iyau kashe mutane da yawa yana ci gaba da haifar da matsaloli musamman ga mata da marayu dake gudun hijira wadanda bar yanzu ba a iya tantance adadinsu ba.

Yanayin da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu a wannan lokacin ya sa suke cike da kwadayin samun tallafi makamancin wannan abin da jagororin al’umma irin mai alfarma Sarkin Musulmi ke ganin ya dace ‘yan siyasa da masu hannu da shuni su shiga gaba wajen samar da irinsa ga jama’ar.

Har iyau dan majalisar ya samar da tallafin daruruwan babura da kekunan dinki da babura masu taya uku domin taimakawa jama’a da rage zaman banza abinda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce ya dace jama’a su daina saka siyasa wajen ceton rayukan mabukata domin acewar sa jama’a dai na ganin cewa da za a ci gaba da samar da irin wannan tallafin da zai iya taimakawa wajen samar da dogaro da kai da kange marasa aikin yi fadawa munanan ayukka.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.