Kaduna Ta Dawo Da Hanyoyin Sadarwa Bayan Hare-Haren Yan Bindiga

A karshe dai gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da bude hanyoyin sadarwar da ta rufe na kusan watanni biyu sai dai ta ce sauran dokokin da aka sa su na nan ba a janye su ba.

WASHINGTON — Tun a watan Okotoba ne dai gwamnatin jahar Kaduna ta bi sahun jahohin Zamfara, Katsina da Sokoto wajen rufe hanyoyin sadarwa da kuma saka wasu dokoki da nufin magance matsalar tsaro sai dai matakin bai hana dauki daidai da ‘yan bindigan ke yi a jahar ba, ko da ya ke kuma kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce rufe hanyoyin sadarwan ya taimaka matuka.

Da yawan al’ummar yankunan da aka fi samun matsalar tsaro dai sun ce rufe hanyoyin sadarwan da kuma matakan tsaro da gwamnatin Kaduna ta dauka ba su sa sun sami sauki ba.

Sai dai kuma Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce duk sauran matakan tsaro da gwamnati ta dauka na nan ba a janye ba.

Dama dai duk da rufe hanyoyin sadarwan da gwamnati ta yi an sami hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan jahar Kaduna domin ko a farkon wannan mako sai da ‘yan bindigan su ka tare hanyar Kaduna-zuwa Abuja da kuma Birnin Gwari zuwa Kaduna, yayin da har yanzu ma’aikatan karamar hukumar Zariyan da aka sace ke hannun ‘yan bindigan.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.