JIHAR KADUNA: ‘Yan-bindiga Sun Sace Dalibai Uku A Makarantar St. Albert

Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ‘yan bindiga suka sako

WASHINGTON, DC — 

‘Yan-bindigan da su ka afka makarantar ta St. Albert tsakanin karfe 7:30 zuwa 8:00 na yamma bayan cin abuncin dare sun bude wuta inda su ka dunga harbe-harbe kafin sace daliban makarantar guda uku.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN reshen jahar Kaduna Rabaren John Joseph Hayeph ya ce wasu daliban da su ka yi gudun ceton rai ma sun ji raunika.

Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.

Wannan hari dai na zuwa ne daidai lokacin da gwamnonin Arewa maso yamman su ka sanya wasu dokoki na bai daya, sai dai masani kan harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai nakasu game da wadannan matakai.Tuni dai ‘yan-bindigan da su ka sace daliban makarantar ta St. Albert su ka kira iyayen su don tattauna kudin fansa, inji shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayeph.

Dama dai rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar da sace daliban har ma mai magana da yawun rundunar ASP Mohammed Jalige ya ce jami’an tsaro sun bi sahu.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.