Ina Da Kwarin Gwiwa Mbappe Zai Ci Gaba Da Zama A PSG – Pochettino

Ita dai Real ta ce a shirye take ta biya fam miliyan 197 don sayen dan wasan dan asalin kasar ta Faransa.

WASHINGTON D.C. — Mai horar da ‘yan wasan Paris Saint Germain Mauricio Pochettino ya ce har yanzu yana da kwarin gwiwar dan wasansa Kylian Mbappe zai sauya shawara ya ci gaba da zama a kungiyar.

Mbappe ya jima yana kokarin barin kungiyar ta PSG inda ya ce tun a watan Yuli ya bayyana musu abin da ke zuciyarsa.

Dan wasan na so ne ya koma kungiyar Real Madrid da ke taka leda a gasar La Liga ta Sifaniya.

A karshen wannan kakar wasa kwantiragin Mbappe zai kare da a PSG.

Rahotanni sun yi nuni da cewa zuwan LIonel Messi da zaman Neymar a PSG za su sa Mbappe ya sauya ra’ayinsa.

Amma duk da haka, dan wasan ya ci gaba da nuna inda hankalinsa ya nufa.

“Za mu yi duk abin da ya kamata don ganin mun rike shi.” Pochettino ya fadawa jaridar El Chiringuito ta kasar Sifaniya kamar yadda Sky Sports ya ruwaito.

Ita dai Real ta ce a shirye take ta biya fam miliyan 197 don sayen dan wasan dan asalin kasar ta Faransa.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.