Ina Cikin Koshin Lafiya – Sadio Mane

Mane ya yi yunkurin cin kwallo ne a lokacin da suka yi gwaren da golan Cape Verde Vozinha, lamarin da ya sa alkalin wasa ya ba golan jan kati.

WASHINGTON D.C. — Dan wasan Senegal Sadio Mane, ya ce babu abin da ya same shi bayan gwaren da suka yi da mai tsaron ragar ‘yan wasan Cape Verde.

Senegal ta doke Cape Verde da ci 2-0 a wasan wanda ya ba ta damar shiga zagayen quarter-finals a gasar AFCON da ake yi a Kamaru.

Mane ya yi yunkurin cin kwallo ne a lokacin da suka yi gwaren da golan Cape Verde Vozinha, lamarin da ya sa alkalin wasa ya ba golan jan kati.

Daga baya dai dole ta sa dan wasan gaban na Liverpool ya fice a wasan inda aka garzaya da shi asibiti saboda buguwar da ya yi.

An dai yi ta nuna fargabar Mane ya samu mummun bugu akan nasa.

Amma daga baya ya wallafa a shafin sada zumunta cewa yana nan kalau kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Gabanin jan katin da aka ba Vozinha, alkalin wasan ya ba Patrick Andrade na Cape Verde jan kati minti 21 da fara wasa, lamarin da ya sa ‘yan wasan na Blue Sharks suka buga wasan da ‘yan kwallo tara kacal.

Mane ne ya fara zura kwallo a ragar Cape Verde a minti na 63 sannan daga baya Bamba Dieng ya kara kwallo ta biyu gab da ana shirin kammala wasan wanda aka yi a zagayen ‘yan 16.

A gefe guda kuma, ita ma Morocco ta bi sahun Senegal wajen shiga zagayen quarter-finals bayan da ta doke Malawi da ci 2-1.

Malawin ce ta fara zura kwallo a ragar Morocco ta hannun Gabadinho Mhango.

Amma daga baya Youssef En-Nesyri ya farke kwallon sannan Achraf Hakimi ya kara ta biyu.

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.