Hukumomin Kasar Jamus Sun Kara Kaimi Wurin Bincike Musabbabin Harin Wuka

Yau Asabar masu bincike a Jamus sun yi kokarin gano musabbabin harin wuka da wani mutum ya kai a birnin Wuerzburg na Jamus inda ya kashe mutane uku da wata doguwar wuka kana ya jikata wasu biyar.
‘Yan sanda sun harbe kana suka kama maharin dan kasar Somalia mai shekaru 24 da haifuwa bayan harin na jiya Juma’a da rana a tsakiyar birnin dake kudancin kasar. ‘Yan sandan sun ce rayuwarsa bata cikin hadari kana ana masa tambayoyi a asibiti.
Wani babban jami’in tsaro yankin Bavari na kasar Jamus, yace ‘yan sanda sun san mutumin kana an kwantar dashi asibitin kula da masu tabin hankali kwanaki kalilan da suka shude. Ya fadawa kamfanin illncin labarai na DPA da yammacin jiya Juma’a cewaba kuma zai fidda batun maharin nada tsaurin ra’ayin Islam aba saboda wani shaidan gani da ido yace ja yi mutumin na kabbara yana cewa Allahu akbar.
Mutumin da ya kai harin yana zaune ne a Wuerzburg tun cikin shekarar 2015, inda galibin gidajen tallafi ga marasa wurin kwana suke. Sai dai bai san mutanen da ya afka musu ba. Mutane sun ajiye furanni kana suka kunna hasken cadir a inda aka kai harin.
Hotunan da aka kafe a shafukan sada zumunta sun nuna masu tafiya da sawu sun gewaye maharin da sanduna da kujeru suna kokari kama shi.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.