Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ci rani ta Najeriya, ta bullo da wani shirin inganta rayuwar ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni daban daban a kasar.
Kwamishinar hukumar Imaan Sulaiman Ibrahim, ta shaida wa BBC cewa, fatan su shi ne su ga cewa wannan rukuni na ‘yan kasa sun zamo masu dogaro da kansu, wanda hakan zai ba su kwarin gwiwar komawa gidajensu nan gaba.
Kwamishinar ta ce akwai hanyoyi da dama da suka bullo da su na taimaka wa ‘yan gudun hijirar ciki har da ba su horo a kan irin sana’oin da suke so.
Ta ce,” Mun hada hannu da wasu hukumomi wadanda za su taimakawa hukumar ta su don ganin an taimakawa ‘yan gudunhijirar su fita daga kangin da suke ciki”.
Imaan Sulaiman Ibrahim, ta ce hukumar NITDA, na daga cikin irin hukumomin da za su taimaka wa hukumar ta su, domin ta ce zata ba wa ‘yan gudun hijirar dubu goma horo a kan sana’oi daban daban.
Kwamishinar hukumar ta ce, da ya ke suna da bayanan ‘yan gudun hijirar, sun san wadanda za su zaba a kan kowacce sana’a da za a koya musu.
Dangane da batun gina wa ‘yan gudun hijirar gidaje a jihohi na Najeriya, ta ce a na su bangaren tuni suka shirye-shirye suka yi nisa,, domin sun kammala gidajen Maiduguri, na Kano kuma an kusa gamawa.
Ta ce, gidajen jihar Katsina da ke Batsari su ma saura kiris a kammala su, saura na Zamfara da Nasarawa da kuma Edo ma da za a fara.
Imaan Suleiman Ibrahim, ta ce a yanzu sun gina gidaje 400 ga ‘yangudun hijira a wadannan jihohi, sannan akwai wasu ma’aikatu da suma za su gina na su gidajen ga ‘yan gudun hijira.
Kwamishinar ta ce akwai bukatar daukacin al’umma su rika taimaka wa gwamnati wurin inganta rayuwar wadannan rukuni na ‘yan kasa, lura da cewa hannu daya baya daukar jinka.
Dubban ƴan gudun hijira a Najeriya na cikin halin yunwa babu wajen kwana mai kyau babu magunguna mai kyau.
Najeriya dai na cikin ƙasashen da suke fama da mutanen da rikici ya raba da gidajensu, musamman ma jihar Borno wadda mahukunta suka ce fiye da mutum miliyan ɗaya ne rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.
-Source:BBCHausa-