Harin jirgin dakon mai: Isra’ila ta ce za a mayar da mummunan martani kan Iran

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Yair Lapid ya dora alhakin harin a kan abin da ya kira ta’addancin Iran

Isra’ila ta zargi Iran da kai hari da jirgin sama maras matuki a kan wani jirgin ruwan dakon mai na wani kamfanin hamshakin attajiri dan Isra’ila, a jiya Alhamis, a gabar ruwan Oman, a tekun Arabia’.

A harin da ya yi sanadiyyyar halakar mutane biyu a cikin jirgin, dan Birtaniya da kuma dan Romaniya, a lokacin da jirgin ke tafiya tsakanin Tanzania da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila ya ce ya gaya wa takawaransa na Birtaniya Dominic Raab za a mayar da mummunan martani.

Duk da cewa zuwa yanzu babu wata tartibiyar sheda karara da ta tabbatar da yadda aka kai harin na ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin jirgin ruwa na Zodiac Maritime na wani hamshakin attajirin Isra’ila Eyal Ofer da ke da cibiya a birnin London, wanda ke tafiyar da jirgin mai suna MV Mercer Street ya nuna,wanda ya ce yana kokarin gano yadda aka kai harin, amma kuma

Isra’ila ba ta yi wata-wata ba ta dora alhakin kai harin a kan Iran, hakan na nunawa karara, yadda yakin sunkuru ko sari-ka-noke da Isra’ila da Iran din ke yi a fakaice, domin ba su fito fili sun ayyana yaki a tsakaninsu ba, yana kara zafafa.

Jirgin dai mallakar Japan ne amma kuma yana dauke ne da tutar Liberia.

Harin wanda aka ce bisa ga dukkan alamu an yi amfani da dan karamin jirgin sama ne da ake sarrafawa daga kasa aka kai shi wanda a lokacin aka kashe biyu daga cikin mutanen cikin jirgin ruwan na dakon mai , dan Birtaniya da dan Romaniya, an kai shi ne a lokacin da jirgin ke tafiya tsakanin Tanzania da Hadaddiyar Daukar Larabawa a gabar Oman a Tekun Arabia.

A wata sanarwa Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Yair Lapid a jiya Juma’a ya dora alhakin harin a kan Iran, yana mai cewa, Iran ba matsala ce ga Isra’ila ba kadai duniya ba za ta yi shiru ba a kai.

A ‘yan watannin na baya-baya, ana kai hare-hare da dama ire-iren wannan a kan jiragen ruwa da ko dai Isra’ila ke tafiyar da su ko kuma Iran, inda kasashen biyu ke zargin juna da kaiwa tare kuma da kin yarda da zargin kusan a kowa ne lokaci.

Sai dai wannan harin na Alhamis a iya cewa ya yi muni ganin cewa har mutum biyu ne suka rasa ransu a lokacinsa.

Abin da ya sa har Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Yair Lapad, ya bukaci da a mayar da mummunan martani, inda ya ce yana tattaunawa da takwaransa na Burtaniya, Dominic Raab. Kuma za a kai maganar gaban Majalisar Dinkin Duniya.

Mai magana da yawun gwamnatin Burtaniya ya ce, gwamnatin na kokarin gaggauta tattara bayanan abin da ya faru.

Duk da gwamnatin Iran ba ta ce komai ba a hukumance, wata tashar talabijin ta Larabci ta kasar ta ruwaito wasu kafofi da ba ta fadi sunansu ba na cewa harin ramuwar gayya ce ta wani hari da ake zargin Isra’ila ta kai kan wani filin jirgin sama a Syria, wadda kawace ga Iran.

Haka ita ma Isra’ilar an ruwaito wani jami’inta da ba a bayyana sunansa ba na cewa abu ne mai wuyar gaske ta kawar da ido a kan harin ba tare da ta rama ba.

-Source: BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.