Ghana Ta Samu Gurbin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya Bayan Doke Najeriya

WASHINGTON D.C. — Ghana ta samu gurbin da za ta kara a gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Qatar a karshen shekarar nan.

Nasarar na zuwa ne bayan da ‘yan wasan Black Stars suka tashi da ci 1-1 da ‘yan wasan Super Eagles a karawar da suka yi a Abuja.

Ghana ta samu wannan dama ce saboda ta bi Najeriya har gida ta zura mata kwallo daya.

A makon da ya gabata, bangarorin biyu suka kara, inda suka tashi canjaras a birnin Kumasi na kasar Ghana.

Dan wasan Ghana Thomas ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya minti 10 da fara wasa.

Sai kyaftin din Najeriya William Troost Ekong ya farke kwallon ta hanyar bugun fenariti, wacce aka ba Najeriya bayan da masu tsaron bayan Ghana suka turmushe Ademola Lookman.

Najeriya ta samu damar zura kwallo ta biyu ta hannun Victor Osimhen, amma alkalin wasa ya soke kwallon bayan da aka gano cewa Osimhen ya yi satar gida.

An kwashe tsawon lokaci bayan da aka dawo daga hutun rabin lokacin bangarorin biyu na kokarin kara kwallo a ragar, musamman Najeriya, amma abin ya ci tura.

Najeriya ta yi canjin ‘yan wasa, amma duk da haka ba ta kai ga gaci ba.

‘Yan wasa irinsu Shehu Abduallahi, Odion Ighalo, Ahmed Musa da Sadiq Umar sun shiga wasan amma haka ba ta cimma ruwa ba.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.