FILATO: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Hudu Wurin Hakar Ma’adinai

Tun bayan kashe wasu ma’aikata hudu a wajen hakar ma’adinai da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Dong dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, al’umman garin suka fara zaman dar-dar sakamakon abun da ka je ya dawo.

ABUJA, NIGERIA. — 

‘Yan bindigar dai sun kai farmaki wurin hakar ma’adinan ne a ranar Asabar da ta gabata, inda suka harbe ma’aikata hudu har lahira, lamarin da ya tilastawa rundunar ‘yan sandan jihar ta tura karin jami’anta zuwa al’ummar da ke fama da zaman dar-dar.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Gabriel Ubah ya fitar a jiya Lahadi, ya ce an tura dakarun ne domin dakile tabarbarewar doka da oda kamar yadda wakiliyarmu a jihar ta shaida maba.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike da nufin kamo wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kuliya a hukunta su.

Baya ga samun labarin afkuwan lamarin, nan take ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru don tabbatar da kare rayukan al’umma in ji, Ubah.

Sai dai ‘yan bindigar da ba a tantance ko su wanene ba, sun kashe mutane hudu da ke aiki a wurin hakar ma’adanai.

A halin yanzu dai gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a yankin da al’amarin ya auku inda jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike domin bankado wadanda suka aikata ta’adin.

Haka kuma, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Bassa a majalisar wakilai ta kasa, Dachung Musa Bagos, ya bayyana kaduwarsa ga yadda rashin samun zaman lafiya ke neman ya zamo abu na yau da kullum a jihar inda ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin mutunta ran dan adam. Ya ce, kamata ya yi gwamnatoci daga tarayya zuwa kasa su dauki matakan gaggawa kan lamarin.

Bagos ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su dauki matakan gaggawa kuma su ba wa hukumomin tsaro umarnin tunkarar matsalar rashin tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.

Rikici tsakanin ‘yan bindiga da wasu al’umman jihar Filato abu ne da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar lamarin da ake samun ramuwar gayya a wasu lokutan kuma, ake ganin ya kamata gwamnati ta sake lale a kai don magancesu baki daya.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.