#EndSARS: Sojoji Sun Bada Bahasi Gaban Kwamitin Bincike

Kwamitin da gwamnatin jihar Lagos ta kafa domin bincike masababin mutuwar wadansu mutane yayinda zanga zangar #EndSARS ya saurari bahasi daga kwamandan rundunar soji da ake zargi da bude wuta kan masu zangar zangar, zargin da rundunar ta musanta.

WASHINGTON, D.C. —  Kwamitin da gwamnatin jihar Lagos ta kafa domin gudanar da bincike bisa zargin bude wuta kan masu zanga zangar kin jinin rundunar ‘yan sanda mai yaki da masu aikata miyagun laifuka, da ‘yan fashi da makami da taken #EndSARS, ya koma zama jiya asabar, bayan shafe mako guda da dakatar da zaman sakamakon janyewar da matasa biyu da ke wakiltar masu zanga zangar suka yi.

Da yake bada bahasi gaban kwamitin bincike mai membobi bakwai da gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya kafa, Kwamandan Bataliya ta 81 na Rundunar sojin Najeriya Brigadiya Janar Ahmed Ibrahim Taiwo, ya musanta yin amfani da karfin soji kan ‘yan zanga zanga a kofar Lekki inda hukumar kare bakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce an kashe mutane goma.

Zanga Zangar #ENDSARS

Brigediya Janar Taiwo ya bayyana cewa, wabiji ne sojoji su shiga lamarin domin kare rayuka da kaddarorin al’umma idan aka sami yanayi na rudani da tashin hankali yadda zanga zangar lumanar #EndSARS ta rikide ta koma tashin hankali. Ya ce an nemi taimakon sojojin ne bayan da lamarin ya wuce kima, mutane suka shiga bata kaddarorin jama’a da kuma kwasan ganima. Bisa ga cewarshi, ana neman taimakon soji a duk fadin duniya idan aka shiga wani hali da ya fi karfin jami’an tsaro, ‘yan sanda da kuma masu kwantar da tarzoma.

Kwamandan sojin ya bayyana takaicin ganin yadda jama’a da suka hada da mata da kananan yara suka shiga wasoson dukiyar wadanda basu ji ba basu gani ba. Ya ce banda taimakawa wajen kwantar da tashin hankalin, rundunar ta kuma taimaka wajen kare kudin ajiya daga bankunan da masu kwasan ganiman suke kokarin fasawa su saci kudi.

endsars-shugaba-buhari-ya-yi-jawabin-kwantar-da-hankali

endsars-matasan-arewa-sun-bukaci-gwamnati-ta-kawo-karshen-zanga-zanga

yadda-zanga-zangar-matasa-ta-janyo-asarar-dukiya-a-jos

Bata gari sun fake da zanga zangar lumanar da aka fara a fadin kasar da nufin neman garambawul a aikin ‘yan sanda, suka shiga wawushe dukiyar jama da kuma lalata kaddarori a birane da dama na kasar musamman a birnin Lagos a zanga zangar da ta kai ga asarar rayuka ranar 20 ga watan Oktoba,

-Source:VOAHausa-

One thought on “#EndSARS: Sojoji Sun Bada Bahasi Gaban Kwamitin Bincike

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.