EFCC Ta Gano Karin Dala Miliyan 72 Da Aka Alakanta Da Diezani

Diezani, na daya daga cikin mashahuran jami’an gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Washington- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta sake bankado wasu makudan kudade da ake alakantawa da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Maduke.

Rahotanni sun ce an gano dala miliyan 72.8 da aka boye a wani asusu a bankin Fidelity.

Bayanai da jaridun Najeriya suka wallafa sun nuna cewa gano kudaden ya sa an kama tsohon Manajan Bankin Nnamdi Okonkwo.

Okonkwo shi ne manajan bankin na Fidelity a lokacin da Maduke ke rike da mukamin ministar man fetur.

A halin yanzu hukumar ta EFCC na tsare da Okonkwo a wani yunkuri na gano inda kudaden suke.

Alison-Maduke, na daya daga cikin mashahuran jami’an gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ta kuma dade tana tserewa hukuma bisa zargin da aka mata na karkata akalar kudaden ma’aikatar man fetur da ta jagoranta.

A baya hukumar ta EFCC ta taba tsare Okonkwo tare da wasu mutane kan wasu kudade da yawansu ya kai dala miliyan 153 da kuma dala miliyan 115 kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce.

Hukumar ta ce tuni dai ta karbo dala miliyan 153 amma har yanzu ba kammala batun dala miliyan 115 ba saboda shari’o’i da ke gaban kotu.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.