Dalilan Farfesa Paiko Na Ficewa Daga Kungiyar ASUU

Farfesa Aliyu Muhammad Paiko na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida mallakar gwamnatin jihar Nejan Nigeria ya yi karin haske akan dalilin da ya sa ya dauki matakin ficewa daga kungiyar malaman Jami’o’in Nigeria ta ASUU.

NIGER, NIGERIA – Kungiyar ASUU dai ta share watanni shida ta na yajin aiki a sakamakon takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnatin Nigeria.

Farfesa Aliyu Paikon dai ya ce bai gamsu ne da dalilan kungiyar ta ASUU ba na yin yajin aiki. Sannan kuma kalaman da shugaban kungiyar ta ASUU na Nigeria ya yi akan malaman da ke koyarwa a Jami’o’i mallakar gwamnatin jihohi.

To kokarin jin ta bakin shugabannin kungiyar malaman reshen Jami’ar ta IBB ya ci tura. Amma daya daga cikin malaman jami’ar ta IBB Dr. Aminu Aliyu Wushishi ya ce matakin da Farfesan ya dauka na ficewa daga kungiyar ta su baya tare da shi.

Bayanai dake fitowa daga hukumar jami’ar ta IBB na cewa an bada umurnin bude makarantar a ranar 5 watan Satumban nan, to amma kuma wata sanarwar daga kungiyar ta ASUU reshen jami’ar ta IBB ta ce suna tare da kungiyar malaman ta Najeriya.

-Source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.