Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanan adadin mutanen da suka kamu da korona kullum a Najeriya, daga ƙididdigar hukumar NCDC. Muna sabunta shi ne da zarar an samu sabbin bayanai kullum.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 251 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.
Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a Abuja suke inda aka samu mutum 78 da suka kamu, sai jihar Legas da aka samu mutum 46, da kuma Kaduna mai mutum 27.
Karin wasu jihohi da cutar ta bulla
- Rivers-21
- Imo-16
- Edo-13
- Delta-12
- Plateau-10
- Niger-7
- Bauchi-6
- Kwara-6
- Akwa Ibom-4
- Benue-3
- Nasarawa-2
A jumullance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 208,404 sai dai 196,123 sun warke.
Akwai kuma mutum2,761 da suka mutu
Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.
Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina – sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi – za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. – akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
-sourceBBCHausa-