Chelsea Ta Sallami Thomas Tuchel

Chelsea ta sha kaye a hannun Dinamo Zagreb da ci 1-0 a gasar zakarun nahiyar turai da aka fara a ranar Talata.

WASHINGTON D.C. — Chelsea ta sallami mai horar da ‘yan wasanta Thomas Tuchel a ranar Laraba, kasa da sa’a 24 bayan da kungiyar ta sha kaye a hannun Dinamo Zagreb.

Sallamar Tuchel na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kungiyar ta kashe makudan kudade da suka kai dala miliyan 300 wajen cefanen sabbin ‘yan wasan.

Chelsea ta sha kaye a hannun Dinamo Zagreb da ci 1-0 a gasar zakarun nahiyar turai da aka fara a ranar Talata.

A gasar Premier League ta kasar Ingila, Chelsea ta sha kaye a wasanninta biyu cikin shida da ta buga inda Leeds da Southampton suka lallasa ta.

Sallamar Tuchel na zuwa ne wata guda da fara kakar wasa ta 2022/2023 inda kungiyar take matsayi na shida a teburin gasar ta Premier.

A shekarar 2021 aka nada Tuchel a matsayin kocin kungiyar bayan da ya horar da kungiyar PSG ta kasar Faransa.

Dan shekara 49, Tuchel shi ne Bajamushe na farko da ya taba horar da kungiyar ta Chelsea.

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.